Tinubu Ya Yi Nade-nade a Hukumomin SEC da NAICOM, 'Yan Arewa Sun Samu Shiga

Tinubu Ya Yi Nade-nade a Hukumomin SEC da NAICOM, 'Yan Arewa Sun Samu Shiga

  • Shugaba Bola Tinubu ya yi sabbin nade-nade a manyan hukumomi guda biyu a yau Juma'a 19 ga watan Afrilu a Abuja
  • Shugaban ya nada Mista Mairiga Aliyu a matsayin shugaban kwamitin hukumar SEC sai Halima Kyari a matsayin shugaba hukumar NAICOM
  • Hadimin shugaban a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale shi ya tabbatar da haka a cikin wata sanarwa da ya fitar a yau

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja - Shugaban kasa, Bola Tinubu ya sake sabbin nade-nade a hukumomin SEC da kuma hukumar inshora ta kasa, NAICOM.

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa sa hidiminsa a bangaren yada labarai, Ajuri Ngelale ya fitar a shafin Facebook a yau Juma'a 19 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Taushen Fage: Al'adar cin nama da sada zumunta da ta shekara sama da 100 a Sakwaya

Tinubu ya nada shugabannin hukumomin SEC da NAICOM
Shugaba Bola Tinubu ya yi wasu sabbin nade-nade a hukumomin NAICOM da SEC. Hoto: Asiwaju Bola Tinubu.
Asali: Facebook

Su waye Tinubu ya ba mukamai?

Mutanen da aka nada a hukumar SEC sun hada da Mista Mairiga Aliyu Katuka a matsayin shugaban kwamitin hukumar sai kuma Emomotimi Agama, babban darekta.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Sauran sun hada da Kasimu Garba Kurfi da Frana Chukwuogor da Bola Ajomale da Samiya Hassan Usman da Lekan Belo.

Sannan a hukumar NAICOM akwai Halima Kyari a matsayin shugabar kwamitin sai Olusegun Ayo Omosehin, kwamishinan inshora da Olawoye Gam-Ikon.

Sauran sun hada da Dakta Usman Ankara Jimada da Dakta Miriam Kene Kachikwu da Adeniyi Olusegun Fabikun da Umar Khalifa Mohammed.

Shawarar da Tinubu ya ba su kan aiki

Tinubu ya bukaci dukkan wadanda suka samu muƙaman da su yi amfani da hikima da kuma tarun ilimin da suke dashi wurin inganta hukumomin.

Shugaban kasar ya kuma bukace su da su samar da wani yanayi da zai karfafawa masu zuba hannun jari gwiwa a ƙasar.

Kara karanta wannan

'Babu wanda zai shigo APC sai da izinin Ganduje,' An ja kunnen Kwankwasiyya

"Tinubu na kaunar 'yan Arewa", Nuhu Ribadu

A baya, kun ji cewa mai ba da shawara kan harkar tsaro ga Shugaba Bola Tinubu, Nuhu Ribadu ya bayyana irin gatan da shugaban ya yi ga mutanen Arewa.

Ribadu ya ce Tinubu ya zabi wasu mukamai masu muhimmanci ya ba yankin domin tabbatar da dakile matsalolinta.

Hadimin ya bayyana haka ne a yau Alhamis 28 ga watan Afrilu a Sokoto inda ya ce shugaban ya san matsalolin yankin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.