Halin kunci: Matasa Sun Sake Kai Hari Kan Motocin Kayan Abincin Tallafi, Sun Tafka Barna

Halin kunci: Matasa Sun Sake Kai Hari Kan Motocin Kayan Abincin Tallafi, Sun Tafka Barna

  • Yayjn da ake cigaba da fama a Najeriya, wasu matasa sun farmaki motoci dauke da abinci guda biyu a jihar Benue
  • Matasan sun kai farmaki kan motocin ne da ke ɗauke da kayan abinci na tallafi zuwa Kudu maso Gabashin kasar
  • Lamarin ya faru ne a Aliade da ke karamar hukumar Gwer a jihar yayin da matasan ke karbar haraji ba bisa ka'ida ba

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Benue - Wasu matasa sun farmaki manyan motoci biyu dauke da kayan tallafin abinci a jihar Benue.

Mukaddashin shugaban hukumar karbar haraji a jihar, Emmanuel Agema shi ya tabbatar da faruwar lamarin.

Kara karanta wannan

InnalilLahi: 'Yan mata sun kwanta dama yayin mummunan hatsarin jirgi, an ceto 3

Wasu matasa sun farmaki motticin kayan abincin tallafi
Matasa a jihar Benue sun kai hari kan motoci 2 dauke da kayan tallafin abinci. Hoto: Nigeria Police Force.
Asali: Facebook

A Ina matasan suka farmaki motocin abinci?

Agema ya ce lamarin ya faru ne a Aliade da ke karamar hukumar Gwer a jihar, cewar rahoton The Nation.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce matasan sun kai farmakin ne kan direbobin da suka ɗauko kayan abincin daga jihar Adamawa zuwa Kudu maso Gabashin kasar.

Ya kara da cewa matasan sun tsayar da direbobin suka faffasa gilasan motar tare da satar kudi N200,000 daga masu motar.

"Miyagun matasan sun dakatar da motocin a wurin karbar haraji da bai halatta ba inda suka fasa gilasan motocin tare da ɗauke kudi kimanin N200,000 daga hannun direbobin."

- Emmanuel Agema

Matakin da hukumomi suka ɗauka kan lamarin

Agema ya ce an yi nasarar cafke mutane biyu da ake zargi da hannu kuma an tura su hukumar DSS bisa umarnin gwamnan jihar.

Ya ce ana can ana bincike tare da zakulo wadanda ke da hannu a karbar haraji ba bisa ka'ida ba a yankin, New Telegraph ta tattaro.

Kara karanta wannan

Daliban jami'ar tarayya ta Gusau da aka sace sun samu 'yanci

Mahara sun farmaki rumbunan abinci a Katsina

A baya, mun ruwaito muku cewa wasu 'yan bindiga sun kai farmaki kan rumbunan abinci na Gwamnatin Tarayya a jihar Katsina.

Lamarin ya faru ne a karamar hukumar Dutsinma da ke jihar kamar yadda hukumar tsaro ta NSCDC ta tabbatar ga manema labarai.

Wannan na zuwa ne yayin da ake yawan samun kai hare-hare kan rumbunan abinci da motoci a fadin kasar baki daya.

Asali: Legit.ng

Online view pixel