NICRAT Ta Kama Hanyar Magance Cutar Sankara Mai Kashe Mutum 78000 a Shekara
- Cibiyar bincike da kula da cutar Sankara ta kasa ta ce a ta samar da wani daftari da zai tattara adadin masu dauke da cutar sankara
- Shugaban cibiyar, Farfesa Usman Malami Aliyu ya tabbatarwa da Legit Hausa cewa samar da daftarin zai taimaka sosai
- Cibiyar ta bayyana cewa a yanzu akwai wuraren dake daukar bayanan masu dauke da cutar a cikin asibitocin kasar nan
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.
Kano - Cibiyar bincike da kula da cutar Sankara ta kasa (NICRAT), ta ce shirye shirye sun yi nisa wajen samar da wani daftari dauke da adadin masu fama da cutar a Najeriya.
A tattaunawar Darakta Janar ɗin hukumar, Farfesa Usman Malami Aliyu da Legit Hausa, ya ce samar da daftarin na bai daya zai taimaka matuka wajen yaki da cutar.
Farfesan a kara bayyana yadda suke kokarin tabbatar da ana bayyana cutar da wuri.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Darakta Janar din ya ce za a yi hakan ne ta hanyar daukar matakan gano cutar da wuri tun daga asibitoci a matakin farko.
Daftarin zai taimaki yaki da Sankara
Farfesa Usman Malami Aliyu ya shaidawa Legit cewa idan aka samar da daftarin na bai daya, zai taimaka matuka.
A karin bayaninsa, Farfesa Usman ya kara da cewa:
"Duk yawancin bayanan da ake akan cutar sankara, kamar ana kiyasi ne na cewa akwai kaza akwai kaza."
"Muna da wuraren tattara bayanan cutar sankara guda 20 wadanda ke cikin asibitoci ."
Darakta Janar ɗin ya ce wadannan ba za su wadata ba, inda ya ce daftarin bai daya zai ba gwamnatin damar fitar da kudi wajen yin bincike a kan cutar.
"Zai taimaka sosai wajen bayar da ainihin adadin masu dauke da cutar a Najeriya."
A cewarsa, za a kuma san wadanne iri aka fi samu a yankunan kasar.
Wani rahoto da The Guardian ta fitar kwanaki ya nuna cutar ta na kashe mutane akalla 78, 000 kowace shekara a Najeria.
An gano riga-kafin cutar Sankara
Binciken masana ya gano cewa dabinon ajwa da ake samu a birnin Madina na dauke da muhimman sinadaran da ke kare mutum daga kamuwa da cutar Sankara.
Binciken da aka gudanar hadin gwiwa wani farfesa na jami'ar Michigan da kuma hukumar bincike ta jami'ar sarki Saud ya gano dabinon na magani a jikin dan Adam kamar yadda magungunan asibiti ke yi.
Asali: Legit.ng