Bincike: An gano cewa akwai maganin cutar daji a jikin dabino

Bincike: An gano cewa akwai maganin cutar daji a jikin dabino

- Sabon bincike yace an gano cewa dabinon Ajwa na Madinah na kunshe da sinadaran hana kamuwa da cutar kansa

- Wannan binciken hadin guiwan anyi shi ne tsakanin wani farfesa na jami'ar Michigan da kuma hukumar bincike ta jami'ar sarki Saud

- Sannanen abu ne cewa dabinon Ajwa na Madinah na da taushi, rashin ruwa da kuma tsada a kasuwannin kasar Saudi Arabia

Sabon bincike yace an gano cewa dabinon Ajwa na Madinah na kunshe da sinadaran dake hana cutar kansa.

Anyi wannan binciken ne a jami'ar King Saud don gano amfanin dabinon Ajwa wanda ya kai masu binciken ga gano amfanin dabinon kamar yadda wasu magunguna irinsu Ibuprofen da aspirin keyi.

Binciken ya gano cewa amfanin dabinon Ajwa daidai yake da magungunan da ake siyarwa a asibiti. An wallafa binciken ne a wata mujallar Amurka wallafa ta 61 ta noma da kimiyyar abinci, wani jami'in KSU ya sanar.

Jami'in yace farfesa Muraleedharan Nair, shugaban dakin bincike na jami'ar Michigan ne yayi binciken hadin guiwar da KSU. Masu bincike da yawa a jami'ar sun taka rawar gani a aikin.

Shugaban sashin bincike na KSU, Saleh A. Aldosari yace wannan ne bincike na farko a jerin binciken da cibiyar ta gudanar a kan dabinon Ajwa wanda ake samu a kasar Saudi Arabia.

KU KARANTA: Ramuwar gayya: Miji yayi zina da abokiyar aikinshi bayan ya gano matarshi na kawo gardi gidanshi

Jami'ar ce ta dau nauyin binciken tare da cibiyar kimiyya da fasaha ta sarki Abdulaziz tare da hukumar tsarin bincike ta masarautar.

KSU ta dau salon binciken kimiyya wanda jami'ar ke daukar nauyi.

An san dabinon Ajwa wanda ake samu a yankin Madinah a masarautar da taushi, rashin ruwa da kuma tsada a kasuwannin Saudi Arabia.

Annabi Muhammad SAW ya bayyana amfani dabinon Ajwa na maganin cutuka daban-daban.

Kamar yadda kwararru a fannin lafiya suka sanar, dabinon Ajwa na kunshe da flavanoid glycosides wanda aka sani da maganin cutuka da yawa.

Sukarin dake cikin dabinon Ajwa na taimakawa masu cutar ciwon sukari.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu:

https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel