Lafiya uwar jiki: Cutar daji (cancer)

Lafiya uwar jiki: Cutar daji (cancer)

Likitoci da masana kimiyya na fadakar da jama'a kan bukatar gudanar da bincike domin gano cutar daji tun da wuri don iya magance ta tun kafin ta samu mazauni a jikin bil'adama, domin hakan shine rigakafi mafi tasiri ga kamuwa da cutar  ta daji.

Lafiya uwar jiki: Cutar daji (cancer)
wani nau'i na cutar daji

Hukumar kiwon lafiya ta duniya wato WHO ta ware ranar 4 ga watan Fabrairu ta kowace shekara a matsayin ranar fadakar da jama'a a kan illar cutar daji ga bil'adama, kungiyar Union for International Cancer Control (UICC) ce ta samar da wannan rana don goyon baya ga cimma manufar littafin cutar daji da aka kaddamar a shekara ta 2008. Hukumar ta lafiya ta ce cutar daji na kashe akalla mutane kusan miliyan 8 a duk shekara.

Matsalar cutar daji, cuta ce da ta gagari likitoci da sauran masana harkokin lafiya a duniya. To sai dai kuma wannan bai hana likitoci da sauran masu dauke da wannan cuta neman magani da kuma bayanai na hana kamuwa da wannan cuta ko kuma maganinta ba a tsakanin bil'adama.

KU KARANTA KUMA: Wani yayiwa kanwarsa fyade

Cutar daji ya kan fito ne kamar kurji ko kumburi, yawancinsu, amma ba wai dole sai ya zama kumburi ba, ma'ananshi shi ne, idan wuri ya jimu, idan ya warke zai daina toho. To shi daji sinadarai ne a cikin jikin mutun kuma sashen jikin mutun ne, wanda maimakon ya daina toho sai ya rika toho ba kai ba gindi, ya zama ya na matse wuri ko kuma ya hana wasu sashen jiki aiki yadda ya kamata. Idan aka tarbe shi yana fitowa, to gaskiya ana iya samun warkarwa amma idan ya yi nisa to sai dai mutuwa"

Ita dai wannan cuta wanda ake ce wa daji, cuta ce wadda idan ta sami wani danuwanka ko wani naka, ba karamin tashin hankali ba ne, daji tayi yawa a yanzu kamar yadda take fitowa yawancin mata a kan nono, wanda har sai a kai ga yanke nonon. Haka kuma akwai cutar daji da dama, wanda suka hada da na kwakwalwa, jini, da dai sauransu.

Lafiya uwar jiki: Cutar daji (cancer)
Dajin nono

Matakin rage yaduwarsu shine da zaran mutun ya fuskanci wani canji a jikinsa ko kurji ya fito masa to ya garzaya zuwa asibitin domin sanin ainahin abunda ke damunsa, ba wai zama a gida ba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel