Rundunar Sojin Najeriya Za ta Ginawa Sojoji Gidaje Bayan Ritaya Daga Aiki
- Rundunar sojin Najeriya za ta samawa sojojin ta da suka yi ritaya gidajen zama.
- Babban hafsan sojojin na kasa, Laftanar Janar Taoreed Lagbaja ne ya bayyana shirin.
- Ya kuma ce rundunar na fitar da sabbin dabarun yaki domin tabbatar da tsarin 'yan Najeriya.
A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa. Abuja- Rundunar sojin kasar nan ta kammala shirin ginawa sojojin dake bakin daga gidaje domin su samu wurin zama bayan sun yi ritaya. A cewar Babban Hafsan sojojin kasar nan, Laftanal Janar Taoreeq Labgaba, rundunar ta kara da ninka kudin inshorar sojojin a wani shirin ko-ta-kwana ba tare da neman karin komai daga jami’an.
Babban Hafsan sojojin ya bayyana hakan a Talatar nan a birnin tarayya, Abuja kamar yadda Daily Trust ta wallafa.
"Muna shirin yaki" Hafsan Sojoji
Laftanal Janar Taoreeq Lagbada ya bayyana cewa rundunar na sabbin shirin yaki domin tunkarar rashin tsaro a sassan Najeriya.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Baya ga fitar da sabbin tsare-tsaren, rundunar za ta kuma karfafawa jami’anta gwiwa domin su ji dadin yake ta'addanci, Leadership News ta ruwaito wannan.
Sojojin ya yi umarnin a ware kaso biyar na gine-ginen ga sojojin da suka samu nakasa yayin aikinsu.
Within Nigeria ta ruwaito cewa tsarin samar da gidajen, musamman ga sojojin da suka samu wata nakasa yayin tabbatar da tsaro a kasar nan zai taimaka wajen inganta yanayin aikin sojojin.
Hafsan sojojin ya tabbatar da cewa rundunar ce za ta dauki nauyi kacokan da samawa jami'anta da za su yi ritaya gidajen.
Rundunar sojin Najeriya na daukar ma'aikata
A watan Janairu mun ruwaito muku cewa rundunar sojin Najeriya ta bayyana fara daukar sabbin sojoji, musamman 'yan gaba da sakandare.
Rundunar ta ce daukar sabbin sojojin zai taimakawa kokarin yakar ta'addanci da rashin tsaro a yankuna daban daban-daban a Najeriya.
A wancan lokaci, daliban da suka kammala sakandare da ke da sha'awar shiga rundunar sojin kasar nan sun ciki komai da ake bukata ne kyauta, kamar yadda rundunar ta sanar.
Asali: Legit.ng