EFCC: An Yi Ta Harbe-harbe Yayin da Gwamnan Kogi Ya Sulale da Yahaya Bello

EFCC: An Yi Ta Harbe-harbe Yayin da Gwamnan Kogi Ya Sulale da Yahaya Bello

  • Rigima ta barke yayin Gwamna Usman Ododo na jihar Kogi ya sulale da mai gidansa, Yahaya Bello bayan hukumar EFCC ta yi wa gidansa ƙawanya
  • Gwamnan ya isa gidan mai tsohon gwamnan bayan hukumar EFCC ta zagaye gidan da nufin kama shi kan zarge-zarge da ake yi kansa
  • Wannan na zuwa ne kwanaki kadan bayan Yahaya Bello ya yi wata ganawa ta musamman da Shugaba Bola Tinubu a fadarsa

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kogi - Yayin da ake ci gaba da kokarin cafke tsohon gwamnan Kogi, Yahaya Bello, Gwamna Usman Ododo ya kawo masa ɗauki.

An gano gwamnan a gidan mai gidan nasa, Yahaya Bello yayin da hukumar EFCC ke kokarin cafke shi a yau Laraba 17 ga watan Afrilu.

Kara karanta wannan

Badakalar N84bn: Kotu ta amince da bukatar hukumar EFCC na cafke Yahaya Bello

Fargaba yayin Ododo ya tsere da Yahaya Bello a gaban EFCC
Gwamna Ododo na jihar Kogi ya sulale da Yahaya Bello yayin da EFCC ke neman cafke shi. Hoto: Alhaji Usman Ododo.
Asali: Facebook

Bello v EFCC: Wane mataki Ododo ya dauka?

An yi ta harbe-harben yayin da gwamnan ya fice daga gidan tsohon gwamnan na Kogi a yau Laraba 17 ga watan Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Daily Trust ta tattaro cewa an gano Yahaya Bello a cikin motar Gwamna Ododo lokacin da yake kokarin fita a gidan.

Wannan dalili ya saka jami'an tsaron da ke dakon tsohon gwamnan suka bude wuta babu ƙaƙƙautawa, cewar rahoton TheCable.

An yi hukunci kan cafke Yahaya Bello

Har ila yau, Babbar kotun jiha da ke zamanta a birnin a Lokoja ta haramtawa hukumar yaƙi da cin hanci da rashawa kamawa, tsarewa da gurfanar da tsohon gwamnan jihar Kogi, Yahaya Bello.

Yayin yanke hukuncin, Mai shari'a I.A Jamil ya yi hukuncin kan kara mai lamba HCL/68/M/2020 ranar Laraba 17 ga watan Afrilu, 2024.

Kara karanta wannan

Gwamna Ododo ya ziyarci gidan Yahaya Bello a Abuja kan abin da jami'an EFCC suka yi

Hukuncin ya biyo bayan zargin tsohon gwamnan kan badakalar N84bn wanda hukumar EFCC ke neman cafke domin amsa tambayoyi.

EFCC ta zagaye gidan Yahaya Bello

A baya, mun kawo labarin cewa jami’an hukumar EFCC sun kai samame gidan tsohon gwamnan jihar Kogi Yahaya Bello da ke unguwar Wuse shiyya ta 4 a babban birnin tarayya Abuja.

Rahotanni sun tabbatar da cewa hukumar ta mamaye gidan ne kwanaki kadan bayan da tsohon gwamnan ya yi wata ganawa da shugaban kasa, Bola Tinubu a fadarsa da ke Abuja.

Wannan na zuwa ne yayin da ake zargin tsohon gwamnan da badakalar kudi har N84bn yayin da ya ke mulkin jihar Kogi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.