Kaduna: Jam’iyyar APC Na Shirin Dakatar da Nasir El-Rufai? Gaskiya Ta Bayyana
- Game da rahotannin da ake yadawa na cewar jam'iyyar APC na shirin dakatar da Nasir El-Rufai, kakakin jam'iyyar na Kaduna ya magantu
- Salisu Wusono, a ranar Talata ya bayyana cewa babu wani shiri na dakatar da El-Rufai, tsohon gwamnan jihar daga jam'iyyar
- A baya-bayan nan ne rahotanni suka rika yawo na cewa APC za ta sallami El-Rufai saboda wasu ayyuka na zagon kasa da yake yi a kasar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kaduna - Jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a Kaduna ta ce babu wani shiri na dakatar da Nasir El-Rufai, tsohon gwamnan jihar.
An samu rahotannin cewa nan ba da jimawa ba za a dakatar da El-Rufai bisa zargin yin ayyukan da suka sabawa jam’iyya.
A wani sako da ya aikawa jaridar TheCable a daren ranar Talata, Salisu Wusono, kakakin jam’iyyar APC a Kaduna, ya ce APC ba ta shirya hakan ba.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
"Babu wannan maganar!" a cewar Wusono.
Wadanne ayyuka ne El-Rufai ya aikata?
A kwanakin baya ne aka ga El-Rufai tare da Abdul Ningi, sanatan da aka dakatar da shi bayan yayi zargin cewa an yi cushe a kasafin kudin shekarar 2024.
Haka kuma jaridar Legit Hausa ta rahoto El-Rufai ya kuma ziyarci hedikwatar jam’iyyar adawa ta Social Democratic Party (SDP) da ke Abuja.
Wadannan ziyarce-ziyarcen sun haifar da cece-kuce a shafukan sada zumunta, a daidai lokacin da ake ta yada jita-jitar cewa tsohon gwamnan na shirin sauya sheka.
El-Rufai ya ziyarci Borno
Ba a wani jima ba kuma sai aka ga tsohon gwammnan na Kaduna ya dura Maiduguri, babban birnin jihar Borno, inda ya gana da Gwamna Babagana Umara Zulum.
A yayin ziyarar, El-Rufai ya yi magana a wani taron karawa juna sani wanda jihar ta shirya, inda ya fallasa gwamnatin Tinubu kan dawo da biyan tallafin fetur.
Har ila yau, a taron ne tsohon gwamnan ya kuma tona asirin yadda wasu gwamnoni ke amfani da wata dabara ta tafka magudin zabe a jihohinsu.
Majalisar Kaduna za ta binciki El-Rufai
Tun da fari, Legit Hausa ta rahoto yadda majalisar jihar Kaduna ta kafa wani kwamiti wanda zai binciki basussuka, kudin tallafi da yadda Nasir El-Rufai ya tafiyar da mulkin jihar.
Kwamitin zai yi duba kan yadda aka karbo kudaden da yadda aka kashe su, da ma tuhumar wani na hannun daman El-Rufai wanda ake zarginsa da almundahana.
Asali: Legit.ng