Jami'an DSS Sun Dauki Mataki Na Gaba Bayan Titsiye Ta Hannun Daman El-Rufai

Jami'an DSS Sun Dauki Mataki Na Gaba Bayan Titsiye Ta Hannun Daman El-Rufai

  • Jami'an hukumar DSS sun saki Aisha Galadima, tna hannun daman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir El-Rufai
  • Aisha ta faɗa komar jami'an hukumar ne bayan an zargeta da yin wasu rubuce-rubuce a kan Gwamna Uba Sani na jihar a watan Fabrairu
  • Ta hannun daman El-Rufai ta yi zargin cewa jami'an DSS masu farare kaya sun muzguna mata tare da lakaɗa mata duka

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

Jihar Kaduna - Jami'an hukumar ƴan sandan farin kaya (DSS) sun saki Aisha Galadima, ta hannun daman tsohon gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir Ahmad El-Rufai.

Tun da farko jami'an DSS sun cafke Aisha ne bisa zarginta da sukar Gwamna Uba Sani na jihar a wani rubutu da ta yi a shafinta na Facebook.

Kara karanta wannan

Malam El-Rufa'i ya bayyana sunan gwamnan da ya fi sauran gwamnoni aiki a Najeriya

DSS ta saki Aisha Galadima
Aisha Galadima ta fito daga hannun jami'an hukumar DSS Hoto: DSS
Asali: Facebook

Sai dai gwamnatin jihar Kaduna ta bayyana cewa ba ta da wata masaniya kan kamun da aka yi wa ƴar siyasar ta jam'iyyar APC.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Babban sakataren yaɗa labaran gwamnan jihar, Muhammad Lawal Shehu, ya bayyana cewa ba su san da batun kama Aisha Galadima ba.

Jaridar Daily Trust ta kawo rahoto cewa an saki Aisha Galadima ne bayan an titsiyeta da tambayoyi na kusan sa'o'i 24.

Wane hali ta tsinci kanta a hannun DSS?

Galadima ta tabbatar da sako ta, inda ta bayyana cewa jami'an DSS sun muzguna mata tare da lakaɗa mata duka, rahoton Politics Nigeria ya tabbatar.

Jigon a jam'iyyar APC mai mulki ta bayyana cewa jami'an na DSS sun zargeta da yin wani rubutu a kan Gwamna Uba Sani a watan Fabrairu.

"Ina ƙoƙarin shiga wanka a ɗakina lokacin da suka zo suka fito da ni waje. Na hango motocinsu na Hilux guda huɗu a wajen gidan. Sun jefa ni a ciki sannann suka tafi."

Kara karanta wannan

Mambobin NNPP sun buƙaci Gwamna Yusuf na Kano ya yi murabus cikin sa'o'i 48, ta faɗi dalili

- Aisha Galadima

El-Rufai ya magantu kan cire tallafi

A wani labarin kuma, kun ji cewa tsohon gwamnan jihar Kaduna, Mallam Nasir Ahmaɗ El-Rufai, ya yi magana kan cire tallafin man fetur a Najeriya.

Tsohon gwamnan na jihar Kaduna ya bayyana cewa har yanzu gwamnatin Tinubu na biyan tallafin man fetur a ɓoye.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng