Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bayar da Tallafin N50,000 Ga Mutanen Najeriya

Tsadar Rayuwa: Gwamnatin Tarayya Ta Fara Bayar da Tallafin N50,000 Ga Mutanen Najeriya

  • Gwamatin tarayya ta sanar da cewa ta fara raba tallafin kudi na 'shirin bayar da tallafi mai dauke da sharadi na shugaban kasa (PCGS)'
  • Ministar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari, Doris Aniete ta bayyana hakan a ranar Talata, inda ta ce tuni aka fara tura kudin
  • 'Yan Najeriya sun yi maraba da wannan tallafi na shugaban kasa, sun roki a gaggauta bayar wa domin ana cikin wani hali

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Ma’aikatar masana’antu, kasuwanci da saka hannun jari ta ce ta fara raba tallafin kudi na shirin PCGS ga 'yan Najeriya.

Shirin PCGS wani tallafi ne da yake karkashin shugaban kasa wanda aka warewa N200bn domin bayar da rance mai sauki ga kananan 'yan kasuwa da masu sana'a.

Kara karanta wannan

CAC: Hukumar kula da kamfanoni ta Najeriya na daukar aiki? Gaskiya ta bayyana

Gwamnatin tarayya ta fara raba tallafin kudi ga 'yan Najeriya
Gwamnati ta ce ba duka wadanda suka nemi tallafin ne za su samu kudin a yanzu ba. Hoto: @officialABAT, @DrDorisAnite
Asali: Twitter

Yaushe za a sake biyan kudin tallafin?

Gwamnati ta hannun bankin masana'antu ta ce za ta raba N200bn din ne a matakai guda uku da kuma dukkanin wadanda suka cancanta su samu kudin.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Doris Aniete, ministar kasuwanci ta wallafa wani rahoto a shafinta na X (Twitter) a ranar Talata tana mai cewa tunin wasu daga cikin wadanda za su gajiyar tallafin suka sami kudadensu.

Aniete ta kara da cewa zuwa ranar Juma'a, 19 ga Afrilu, za a sake biyan kudin ga wani adadi mai yawa na wadanda aka tantance.

Kowa zai samu tallafin gwamnatin?

Ta ce:

"An fara bayar da kuɗin 'shirin bayar da tallafi mai dauke da sharadi na shugaban kasa'. Ana ci gaba da tsare-tsare kuma tuni wasu masu cin gajiyar tallafin sun sami kudinsu.
"Yana da muhimmanci a fahimci cewa ana ci gaba da biyan kuɗin ne yanzu, kuma ba duk masu neman tallafin ba ne za su sami kudin a wannan rabon na farko."

Kara karanta wannan

Yan ta'adda sun halaka sojoji da dama a wani mummunan kwanton bauna

Duk da hakan, ministar ta bayar da tabbatacin cewa duk masu neman tallafin da aka tantance za su samu kudin su a matakai na gaba

Legit Hausa ta ji ta bakin jama'a

Bullar wannan rahoto ke da wuya, Legit Hausa ta zagaya jihar Kaduna, domin jin ra'ayoyin jama'a kan wannan yunkuri na gwamnati.

Kabiru Maigawayi ya ce ya ji dadin yadda aka fara rabon tallafin, domin ya dade da nema kuma ya sabunta bayanansa da NIN.

Ko da aka tambaye shi amfanin da tallafin zai yi masa, Kabiru ya ce:

"Zan bunkasa sana'a ta. Tallafin 50,000 zai taimaka na karo buhunan gawayi da dama, ka ga nima iyalina za su iya ganin canji a cefane."

A bangaren mata masu sana'a a cikin gida, mun zanta da Malama Zainab Makarfi, wadda ke sayar da gyada 'ta soyu'.

"Ni dai ina addu'ar Allah ya sa kudin nan in same su da wuri domin ina cikin mawuyacin hali. Ko cefanen kirki yanzu mun daina yi, don ma Allah ya sa muna sana'ar."

Kara karanta wannan

Tashin farashin Dala: Kokarin da CBN yake yi na daidaita Naira a kasuwar canji

"Wahalar da ke tunkarar Najeriya" - Ayodele

A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa babban malamin addinin Kirista, Primate Ayodele ya ce ya hango wahalar rayuwa da ake tunkarar Najeriya.

Ayodele ya ce har sai gwamnatin Bola Ahmed Tinubu ta dauki matakin gaggawa kan tattalin arziki ne za a iya kare faruwar hakan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.