Gwamnatin Jihar Gombe Ta Dawo da Dokar Sharar Wata Wata

Gwamnatin Jihar Gombe Ta Dawo da Dokar Sharar Wata Wata

  • Gwamnatin jihar Gombe ta sanar da dokar sharar gama gari da za a rika yi duk ranar Asabar din karshen wata a fadin jihar
  • Dokar zata fara aiki ne a karshen watan Afrilu kuma za a rika daukan awa biyu ana gudanar da sharar ba tare da barin zirga-zirgar al'umma ba
  • Gwamnatin ta yi kira ga daukacin al'ummar jihar da su yi iya kokari wurin bada hadin kai ga hukumomi domin tabbatar da tsaftace jihar baki daya

Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.

Jihar Gombe - Gwamnan jihar Gombe, Alhaji Muhammadu Inuwa Yahaya, ya amince da dawo da dokar sharar gama gari duk ƙarshen wata.

Kara karanta wannan

Innalillahi: An yi wa yarinya 'yar shekara 10 kisan gilla a wani birnin Arewacin Najeriya

Gwamnan ya sanya ranar Asabar din karshen kowane wata a matsayin ranar da za a rika sharar domin tabbatar da tsaftar muhalli.

Inuwa Yahaya
Gwamna Inuwa ya dawo dokar shara kowane wata a Gombe. Hoto: Isma'ila Uba Misilli
Asali: Facebook

A cewar sanarwar, an saka dokar ne ta domin tabbatar tsabtar muhalli da kyautata lafiyar al'ummar jihar Gombe.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Yaushe za a fara share Gombe?

Wata sanarwa da mai taimakawa gwamnan a harkar yada labarai, Isma'ila Uba Misilli, ya rubuta a shafinsa na Facebook ta nuna cewa za a fara sharar ne daga karshen watan Afrilu.

Sanarwar ta bayyana cewa za a riƙa gudanar da aikin tsabtace muhallin ne daga ƙarfe 8.0 na safe zuwa 10.0 na safe.

Kuma za a aiwatar da dokar taƙaita zirga-zirgar jama'a da ababen hawa, sai dai ga mutanen dake aiwatar da muhimman ayyuka.

Kira ga al'ummar jihar Gombe

Sanarwar ta kara da cewa ana umurtar dukkan ma'aikatu da hukumomin gwamnati da sauran jama’a su bi umarnin, domin tawagar jami’an gwamanti da hukumomi za su sanya ido sosai don tabbatar da bin wannan umarni.

Kara karanta wannan

Daliban jami'ar tarayya ta Gusau da aka sace sun samu 'yanci

An tsawaita hutun sallah a Gombe

Haka zalika kun ji cewa gwamna Muhammed Inuwa Yahaya ya tsawaita hutun karamar sallah har zuwa ranar Jumu'a, 12 ga watan Afrilu, 2024 a jihar Gombe.

Gwamnan ya ɗauki wannan matakin ne domin bai wa mutanen jihar damar ci gaba da bukukuwan sallah ba tare da tunanin komai ba.

Asali: Legit.ng

Authors:
Ibrahim Yusuf avatar

Ibrahim Yusuf (Hausa Editor) Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum. ibrahim.yusuf@corp.legit.ng