Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Suna Can Sun Kai Hari a Jihar Neja

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Suna Can Sun Kai Hari a Jihar Neja

- Wasu yan bindiga da ba a san ko su wanene ba sun kai hari kauyen Tegina a jihar Niger

- Majiyoyi da dama sun tabbatar da cewa maharan sun shiga garin a kan babura suna ta harbe-harbe

- An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun yan sandan jihar Niger amma abin ya ci tura

'Yan bindiga suna can sun hai hari a kauyen Tegina da ke karamar hukumar Rafi a jihar Niger kamar yadda The Nation ta ruwaito.

Majiyar Legit.ng ta tattaro cewa yan bindigan sun afka babban garin na Tegina suna ta harbe-harbe.

Wata majiya daga hukumomin tsaro ta ce mutanen gari sun buya domin tsaron kada harsashi same su.

DUBA WANNAN: Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Sun Kashe Ahmed Gulak, Tsohon Hadimin Goodluck Jonathan

Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Suna Can Sun Kai Hari a Jihar Neja
Yanzu-Yanzu: 'Yan Bindiga Suna Can Sun Kai Hari a Jihar Neja. Hoto: @TheNationNews
Asali: UGC

Wasu majiyoyin sun tabbatar da afkuwar lamarin suna mai cewa yan bindigan sun mamaye hanyar Tegina-Zungeru-Minna suna tsare motocci suna musu fashi.

An yi kokarin ji ta bakin mai magana da yawun rundunar yan sandan jihar Niger amma bai amsa wayarsa ba.

Kazalika, Sanata Shehu Sani, tsohon sanata mai wakiltar mazabar Kaduna ta tsakiya shima ya tabbatar da harin.

KU KARANTA: Bahaushen Da Ya Riƙe Amanan Bayarabe Tsawon Shekaru 30 Ya Sha Yabo

A cikin rubutun da ya wallafa a shafinsa na Twitter, Shehu Sani ya ce wani mai sarautar gargagjiya ta tabbatar masa cewa yan bindiga sun afka garin na Tegina a jihar Niger.

Ya ce sun zo da muggan makamai sun sace mutane sun tafi da su cikin daji.

"Wani mai sarautar gargajiya a yankin ya sanar da ni cewa mintuna 30 da suka shude yan bindiga sun afka kauyen Tegina a jihar Niger. Sun zo kan babura da muggan makamai kuma sun sace mutane sun tafi da su daji. Mutanen garin da dama yanzu suna fitowa daga inda suka buya," a cewar Shehu Sani.

A wani labarin daban, 'yan sanda a birnin tarayya Abuja sun kama Ahmad Isah, mai rajin kare hakkin bil adama kuma dan jarida, saboda shararawa wata mari da ake zargi da cin zarafin wata yarinya.

Isah, wanda aka fi sani da 'Ordinary President' ya dade yana gabatar da wani shirin rediyo da talabijin mai suna "Brektet Family".

Al'umma sun yi korafi a kansa ne bayan an gan shi cikin wani faifn bidiyo da BBC Africa Eye ta wallafa yana marin wata mata da ake zargin da cinnawa yar dan uwanta wuta a kai kan zarginta da maita.

Asali: Legit.ng

Online view pixel