Gwamnatin Tinubu Ta Tsoma Baki Kan Rikicin Iran da Isra'ila

Gwamnatin Tinubu Ta Tsoma Baki Kan Rikicin Iran da Isra'ila

  • Gwamnatin tarayya ta yi kira ga ƙasashen Iran da Isra'ila da su sanyawa zukatansu ruwan sanyi biyo bayan harin da aka kai a ranar Asabar 13 ga watan Afrilu
  • A cikin wata sanarwa a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu, gwamnatin ta hannun ma'aikatar harkokin wajen ƙasar, ta ba da shawarar hanyar warware rikicin cikin lumana
  • Gwamnatin da Tinubu ke jagoranta ta tunatar da ƙasashen da ke rikici da juna da su mayar da hankali wajen tabbatar da zaman lafiya

Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi

FCT, Abuja - A yayin da ci gaba da rikici tsakanin Iran da Isra’ila, ƙasashe musamman na yammacin duniya sun yi kira da a tsagaita buɗe wuta.

Kara karanta wannan

Yadda 'yan matan Chibok suka dawo da yara 34 bayan Boko Haram sun sako su

Ƙasashen sun kuma yi kira da a hau teburin sulhu domin kawo ƙarshen rikicin da ke neman ƙara yaɗuwa.

Gwamnatin tarayya ta yi magana kan fadan Isra'ila da Iran
Gwamnatin Tinubu ta bukaci Iran da Isra'ila su zauna lafiya Hoto: @DOlusegun, @netanyahu
Asali: Twitter

A nata ɓangaren, gwamnatin tarayyar Najeriya ta bakin ma'aikatar harkokin wajen ƙasar nan ta buƙaci ƙasashen Iran da Isra'ila da su yi haƙuri da juna.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Me gwamnatin Tinubu ta ce kan rikicin?

Gwamnatin ta buƙaci hakan ne domin gujewa ɓarkewar rikici a yankin Gabas ta Tsakiya.

Hakan na ƙunshe ne a cikin wata ƴar gajeruwar sanarwa a X da ma'aikatar ta fitar a ranar Lahadi, 14 ga watan Afrilu mai ɗauke da sa hannun kakakinta, Fransisca Omaluyi.

Ma’aikatar ta bayyana cewa, a cikin wannan lokaci, ya zama wajibi ƙasashen biyu su yi tunani a kan ƙudurin da ƙasashen duniya suka ɗauka na warware rikice-rikice cikin lumana domin ci gaban zaman lafiya da tsaro a duniya.

Kara karanta wannan

Gwamnatin Borno ta sha alwashin ceto ragowar 'yan matan Chibok da ke hannun Boko Haram

Wani ɓangare na sanarwar na cewa:

"Gwamnatin tarayyar Najeriya ta bi sahun sauran ƙasashen duniya wajen yin kira ga Iran da Isra’ila da su yi taka-tsantsan, yayin da ake ci gaba da ƙoƙarin diflomasiyya na kwantar da hankula da kaucewa ɓarkewar rikici a Gabas ta Tsakiya."

Amurka ta raba gari da Isra'ila

A wani labarin kuma, kun ji cewa shugaban ƙasar Amurka ya nesanta kansa kan shiga cikin Iran da Isra'ila.

Joe Biden ya bayyana cewa Amurka ba za ta taimakawa Isra'ila ba ta kai hari kan ƙasar Iran a rikicin da ƙasashen biyu ke yi.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sharif Lawal avatar

Sharif Lawal Sharif Lawal ma'aikacin jarida ne wanda ya samu gogewa a harkar aikin jarida. Ya yi digirinsa na farko a jami'ar Ahmadu Bello (ABU) da ke Zaria. Ya samu horo daga Reuters kan aikin jarida da tantance labarai. Za a iya tuntubarsa ta Sharif.lawal@corp.legit.ng