Ya Kamata Najeriya ta Nemi Kwastomomin Gurbataccen Manta a Afrika, Masani

Ya Kamata Najeriya ta Nemi Kwastomomin Gurbataccen Manta a Afrika, Masani

  • Masanin ma'adanai a Najeriya ya shawarci gwamnati ta sauya dabarar kasuwancin man fetur din ta take hakowa
  • Injiniya Haruna Yusuf Beli, Ubandoman Rogo ya ce rashin kasuwancin gurbataccen man fetur din a Nahiyar Afrika zai jawo matsala
  • Rahoton Bloomberg ya bayyana yadda Najeriya ta gaza sayar da danyen man fetur din da ta hako a baya

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

A'isha Ahmad edita ce a sashen Hausa na Legit. Tana da ƙwarewa wajen rubutun labarai da rahotanni tsawon shekaru uku. Ta kware a kawo rahotannin, al'amuran da su ka shafi mata da yara da siyasa.

Najeriya- Masana a ɓangaren ma'adanan man fetur sun shawarci gwamnatin Najeriya ta fara kasuwancin gurɓataccen man da take haƙowa a Nahiyar Afrika da gaske, domin gujewa yin bandaro nan gaba a kasuwar duniya.

Wani rahoton Bloomberg ya ce har yanzu akwai gurɓataccen man da Najeriya ta fitar sau ashirin zuwa ashirin da biyar da har yanzu ba ta sayar ba.

Kara karanta wannan

Tsohon gwamna Malam El-Rufa'i ya bayyana babbar matsala 1 tak da ta addabi Najeriya

Man fetur
Masanin ya ce Najeriya ta fi sauran kasashe samar da danyen man fetur mai saukin tacewa Hoto: nnpcgroup.com
Asali: UGC

Kuma kowane kaya da aka fitar aƙalla na ɗauke da gangar ɗanyen mai miliyan ɗaya, kamar yadda TheCable ta wallafa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A hangen masana, irin su Injiniya Haruna Yusuf Beli Ubandoman Rogo, rashin kasuwancin danyen man fetur ɗin a nahiyar Afrika na daga dalilan da ya sa ta ke halin da take ciki.

"Musamman saboda masu sayen man Najeriya ƙasashen Turai ne da wasu ɓangare na Asia."

A cewar Injiniya Ubandoman Rogo yajin aikin ma'aikata a ƙasashen Spain da Faransa ya rage buƙatar gurɓataccen man da Najeriya ke fitarwa.

"Wasu ƙasashen Turai za su rufe matatun mansu, kin ga idan matatun mai ba su yi aiki ba, babu yadda za a yi a nemi gurɓataccen mai a zo a sarrafa shi.

A fara sarrafa mai a cikin gida

Injiniyan ya shaidawa Legit Hausa cewa gurɓataccen man fetur da ƙasar nan ke haƙowa yana da kyau da sauƙin tacewa idan aka haɗa da na sauran ƙasashen duniya.

Kara karanta wannan

An samu tashin mummunar gobara a babbar kasuwar jihar Adamawa

Saboda haka yake ganin kamata ya yi Najeriya ta samu kasuwa a Afrika domin kaucewa bandaro da ɗanyen man ke yi idan an samu akasi irin wannan.

"Sannan kuma refineries ɗinta na cikin gida, su gyaru, a gyara su, ya zamo mu ma za mu dinga fitar da shi."
"Musamman ga ta Ɗangote ɗin nan ta zo," inji shi.

Masanin yana ganin samun kasuwar gurɓataccen man a cikin gida zai magance yiwuwar ƙara faɗawa matsalar tattalin arziƙi a Najeriya.

An gina gidan mai don karya farashinsa

Kamfanin iskar gas din NIPCO ya kammala shirin bude gidajen mai da ake sa ran zai sayar da mai cikin farashi mai rahusa.

Gidajen mai hudu kamfanin ya kammala ginawa kuma za su fara aiki a karshen watan nan.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Ahmad avatar

Aisha Ahmad (Hausa editor) Edita ce a sashen Hausa na legit.ng. Ta samu horon aikin jarida, musamman ta bangaren tace labarai a Premier Radio, da ICIR, da Express Radio. Ta shafe sama da shekaru goma tana aikin ɗaukar rahoto a jihar Kano.