Wata daliba a jihar Sakkwato ta kashe jaririnta dan gaba da fatiha
Wata budurwa mai shekaru goma sha tara, 19, a rayuwa, ta hallaka dan jaririn da ta haifa dan gaba da fatiha, watau ba ta hanyar aure ta haife shi ba, ta hanyar dode masa hanci ta hana shi shaker iska, inji rahoton jaridar Daily Trust.
Budurwar mai suna Munirat Basna, wanda daliba ce a kwalejin horas da jami’an kiwon lafiya dake jihar Sakkwato ta shiga hannun Yansanda ne a ranar Alhamis, 7 ga watan Mayu sakamakon laifin da ake zarginta da aikatawa.
KU KARANTA: Yaki da ta’addanci: Gwamnatin Amurka ta sanar da antaya ma Najeriya dala miliyan 102
Kaakakin rundunar Yansandan jihar Sakkwato, DSP Cordelia Nwawe ta bayyana ma majiyar Legit.ng cewa bayan Munirat ta tabbatar jaririn nata ya mutu, sai ta jefar da gawarsa a cikin kwandon shara.
Da take yi ma manema labaru jawabi, Munirat tace cikin shege ta yi, kuma ba ta san wanene Uban yaron ba, bugu da kari ma jaririn bakwani ne, a cewarta. Sai dai Kaakaki Nwawe tace zasu mika Munirat gaban Kotu da zarar sun kammala bincike.
A wani labarin kuma, rundunar Yansandan jihar ta kama wani matashi mai suna Nnamdi Nwosu da laifin satar motoci, inda tace barawon ya kware wajen zuwa neman manyan Motoci Coci, kuma Yansanda sun kwato wata Mota kirar Marsandi daga wajensa.
Ku biyo mu a https://www.facebook.com/naijcomhausa
ko a http://twitter.com/naijcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.ng Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng