Hadiza Balarabe: Mace ta farko da aka fara zaba mataimakiyar gwamna a Kaduna

Hadiza Balarabe: Mace ta farko da aka fara zaba mataimakiyar gwamna a Kaduna

Dr Hadiza Balarabe itace mataimakiyar gwamna na biyu a tarihin jihar Kaduna amma itace zababiyar mataimakiyar gwamna na farko a tarihin jihar.

Tayi nasarar zama mataimakiyar gwamna ne a zaben da aka gudanar bayan an zabe ta a matsayin abokiyar takarar gwamna Nasir El-Rufai da ke neman zarcewa a kan mulki karo na biyu inda mutane da dama suka rika murnar lashe zabenta a kafofin sada zumunta.

Kafin zaben Hadiza, an kwashe shekaru 17 a jihar ba tare da zaben mace a matsayin mataimakiyar gwamna ba. An samu mataimakiyar gwamna mace ne a shekarun 90's kuma shekaru biyu kacal tayi a mulki wato (1990-1992).

DUBA WANNAN: Kiri da muzu: An ga wakilan PDP na rabawa masu zabe kudi a Abuja

An nada Abubakar Ayuba a matsayin gwamnan mulkin soji na jihar Kaduna tare da Pamela Saduki a matsayin mataimakiyarsa. Saduki ce mace na farko a tarihin jihar da ta taba zama mataimakiyar gwamna.

Hadiza Balarabe ce mace ta farko da ta aka zaba mataimakiyar gwamna a tarihin jihar.

An dai haife Dr Hadiza Balarabe na a 1966 a karamar hukumar Sanga na jihar Kaduna. Tayi karatun likita a Jami'ar Maiduguri kafin daga bisani ta fara aiki da Asibitin Koyarwa na Jami'ar Ahmadu Bello da ke Zaria kafin a 2004 ta koma aiki a Abuja.

Dr Hadiza Balarabe ce babban sakataren cibiyar kula da lafiya bai daya na jihar Kaduna tun a watan Fabrairun 2016.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Online view pixel