2023: El-Rufai ya zabi wanda yake so ya zama Magajinsa a cikin manyan na-kusa da shi

2023: El-Rufai ya zabi wanda yake so ya zama Magajinsa a cikin manyan na-kusa da shi

  • Gwamnan jihar Kaduna ya ayyanawa na-kusa da shi wanda yake sha’awar ya zama ‘dan takara
  • Malam Nasir El-Rufai ya tafi da Sanata Uba Sani, watakila Dattijo ba zai samu kai labari a 2023 ba
  • El-Rufai ya dauki wannan matsaya ne bayan ya dauki tsawon lokaci yana wata tattaunawa a jiya

2023 - Mai girma gwamnan jihar Kaduna, Malam Nasir El-Rufai ya zabi Sanata Uba Sani a matsayin wanda yake so ya zama ‘dan takarar gwamna a APC.

Daily Trust ta samu labari cewa Malam Nasir El-Rufai ya dauki wannan matsaya ne bayan dogon tattaunawa da nazari a kan masu neman kujerar gwamna a 2023.

A wajen wannan zama da aka yi a ranar Laraba, 4 ga watan Mayu 2022, Mai girma gwamna El-Rufai ya nunawa ‘yan siyasar na jihar Kaduna inda ya sa gaba.

Kara karanta wannan

‘Dan shekara 47 mai ji da kudi ya saye fam din APC, zai yi takarar Shugaban kasa a 2023

Jaridar ta samu wani sako da ya tabbatar da hakan da daya daga cikin masu neman takarar ya aika.

“Mun yi zaman a kusan awanni uku. Kowa ya yarda cewa a kyale Malam ya yi yadda yake so. Ya zabi Uba a matsayin ‘dan takara.”
“Dole mu karbi wannan a matsayin yin Allah domin gujewa surutai daga baya. Bari mu ga yadda za mu shawo kan magoya bayanmu.”

- Wani daga cikin masu neman takara

El-Rufai da Sanatocin APC
Gwamna El-Rufai, Sanata Kwari da Uba Sani Hoto: @ubasanius
Asali: Facebook

Ina matsayar Dattijo?

Har ila yau, rahoton ya bayyana cewa El-Rufai ya fadawa tsohon Kwamishinansa, Muhammed Sani Abdullahi ya nemi takarar Sanatan Kaduna ta tsakiya.

Malam Muhammed Sani Abdullahi wanda aka fi sani da Dattijo ake so ya gaje kujerar Uba Sani.

Kafin yanzu Dattijo yana cikin wadanda ake tunani zai iya zama ‘dan takarar Gwamna. A ranar Juma’ar nan ya yi niyyar ya yanki fam din neman takara.

Kara karanta wannan

Takaitaccen tarihin Uba Sani wanda El-Rufai yake goyon bayan ya karbi Gwamna a 2023

Uba Sani ne damun Malam?

A yadda abubuwa su ke tafiya, Sanatan Kaduna ta tsakiya shi ne zai yanki fam a cikin manyan na kusa da gwamna domin ya yi takara a babban zabe mai zuwa.

Kafin zamansa Sanata a zaben 2019, Uba Sani shi ne mai ba gwamnan jihar Kaduna shawara a kan harkokin siyasa, ya dade yana tare da Malam El-Rufai.

Siyasar Kano

A gefe guda kuma ku na da labari cewa akwai mutane fiye da 10 da alamu suka nuna cewa za su iya neman takarar kujerar gwamna a jihar Kano a zaben 2023.

Wadanda ake tunanin za su iya kai labari sun hada da: Sha’aban Ibrahim Sharada, Abba Kabir Yusuf, Murtala Sule Garo, Inuwa Waya da Sanata Barau Jibrin.

Asali: Legit.ng

Online view pixel