Jami'ar Ibadan t shiga jerin mafi ingantattun jami'oi 1000

Jami'ar Ibadan t shiga jerin mafi ingantattun jami'oi 1000

Wata jerin ingantattun jami'o'i da Times Higher Education ta yi ta sanya jami'ar Ibadan a matsayin na 801 cikin 978 na mafi ingantattun jami'o'i a fadin duniya, ita kadai ce jami'ar Najeriya da ta samu shiga cikin jerin.

Jami'ar Ibadan t shiga jerin mafi ingantattun jami'oi 1000

Kafin wannan lokacin, babu jami'ar najeriyan da ta taba shiga jerin mafi ingantantun jami'o'i 1000 a duniya kuma ana ganin rashin yin bincike ne ya kawo hakan.

Jami'ar Oxford ce na daya a jerin , ta doke California Institute of Technology,wacce tayi shekara 5 tana zuwa na daya, amma ta zo na biyu yanzu. Ana jingina nasarar Oxford zuwa ga abubuwa 4 wadanda sune , koyarwa,bincike, da sauran su.

Bugu da kari, abin da jami'ar ke yi na bincike ns fin yawan malamanta, bincike ta yafi amfani, kuma an fi amfani da shi a duniya.

KU KARANTA: Jam’iyyar APC ta aika sunan Akeredolu INEC a matsayin dan takaran ta

Rahoton ta nuna cewa jami'o'in nahiyar asiya 2 ne suka samu shiga 100 farko (Chinese University of Hong Kong and Korea Advanced Institute of Science and Technology (KAIST).

Kana City University of Hong Kong, University of Science and Technology of China, Fudan University and Hong Kong Polytechnic University ,sun shiga cikin dar biyun farko.

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng