Ganduje: Yayin da Ake Cece-kuce, Abba Ya Fayyace Gaskiya Kan Kafa Kwamitin Bincike
- Yayin da ake ci gaba da binciken Dakta Abdullahi Ganduje, Gwamna Abba Kabir ya fayyace dalilin daukar matakin
- Abba ya ce bai kafa kwamitin binciken domin bita da kullin siyasa ba sai dai domin tabbatar da gaskiya a gudanar da gwamnati
- Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya kafa kwamitin bincike kan shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Umar Ganduje
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir ya yi martani kan binciken tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Gwamnan ya ce ko kadan babu bita da kullin siyasa kan binciken badakalar kadarorin gwamnatin jihar, cewar Daily Trust.
Musabbabin kafa kwamitin da Abba ya yi
Abba Kabir Yusuf ya bayyana haka ne yayin karbar bakwancin Sarkin Kano, Aminu Ado Bayero a gidan gwamnati bayan ya kawo ziyarar gaisuwar sallah.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Gwamnan ya ce ya kafa kwamitin ne domin tabbatar da gaskiya da kuma neman hanyar dakile rikicin siyasa a jihar da ya faru a baya.
Ya kuma sha alwashin cewa zai yi dukkan mai yiwuwa domin daukar mummunan mataki kan masu ingiza rikicin siyasa ko da kuwa daga wace jami'yya ce.
Godiya da Sarkin Kano ya yi ga Abba
Tun farko a jawabinsa, Sarkin Kano ya ce sun zo gidan gwamnatin ne domin gaisuwar sallah ga gwamnan a yau Juma'a 12 ga watan Afrilu.
Sarkin ya yabawa gwamnan kan irin ayyukan alheri da ya kawo a jihar domin ci gaban al'umma, a cewar rahoton New Telegraph.
Ya shawarci iyayen yara dasu tabbatar sun ba 'ya'yansu kulawa da tarbiyya domin dakile matsalar dabanci a siyasar jihar.
Kungiya ta ja kunnen Abba kan Ganduje
A baya, mun kawo muku labarin cewa wata kungiyar a jihar Kano ta ja kunnen Gwamna Abba Kabir kan binciken shugaban jam'iyyar APC, Dakta Abdullahi Ganduje.
Kungiyar mai suna Arewa Renaissance Front ta ce Ganduje bai tsoron komai saboda ayyukan alheri da ya yi a jihar.
Wannan na zuwa ne bayan Gwamna Abba Kabir ta kafa kwamitin bincike kan tsohon gwamnan jihar, Dakta Abdullahi Umar Ganduje.
Asali: Legit.ng