Tsadar Rayuwa: Gwamnan Arewa Ya Yi Abu 1 da Ya Faranta Ran Ma’aikatan Jiharsa
- Kwamishinan yada labarai na jihar Jigawa, Sagir Musa ya ce gwamnatin jihar ta sake daukar matakin saukaka wa rayuwar ma'aikatan jihar
- Sagir Musa ya bayyana ce jihar ta ware Naira biliyan 1.1 domi sayen kayan abinci wanda za ta sayarwa ma'aikata kan farashi mai rahusa
- Wasu daga cikin mazauna jihar Jigawa da Legit Hausa ta zanta da su, sun yabawa gwamnan bisa kokarin da yake yi kan ma'aikatan jihar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Jigawa - Gwamnatin jihar Jigawa ta ware Naira biliyan 1.1 domin siyan karin kayan abinci na gaggawa da za a sayarwa ma'aikatan jihar.
Kwamishinan yada labarai, matasa, wasanni da al’adu, Sagir Musa ne ya bayyana haka yayin da yake zantawa da manema labarai a jiya Alhamis.
Kayan abinci da za a ba ma'aikata
Sagir Musa ya ce gwamnati ta cimma wannan matsayar ne a taron majalisar zartarwa da ya gudana a ranar Litinin da nufin saukakawa ma'aikatan kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kayayyakin da za a siya sun hada da buhunan shinkafa 12,000 da katon 15,000 na taliya, wanda za a sayarwa ma’aikatan gwamnatin kan farashi mai rahusa.
Ya ce siyan kayan abincin na cikin shirin gwamnatin jihar na samar da shaguna na hadin gwiwa a dukkan kananan hukumomi 27 na jihar.
"Ma'aikata za su iya karbar bashi" - Musa
Jaridar Leadership ta rahoto kwamishinan na nuni da cewa za ayi amfani da shagunan a matsayin wuraren da ma'aikatan jihar za su rika sayen kayan abinci a farashi mai rahusa.
Sagiru ya ce tuni aka samar da hanyoyin kafawa da sarrafa shagunan hadin gwiwar inda ma’aikata za su iya karbar kayan abinci a kan bashi da kuma biyan kudin kadan-kadan.
Kwamishinan ya kara da cewa an kashe N2.8bn a shirin ciyar da al'uma abinci a watan Ramadan na bana.
Gwamna Namadi na kokari - Bamai
Kwamared Bamai Dabuwa da Legit Hausa ta ji ta bakinsa kan wannan lamari ya ce Gwamna Umar Namadi na daga cikin gwamnonin da Jigawa ta yi dace da su.
Ya ce tun bayan hawan gwamnan mulki yake fitar da tsare-tsare da za su kawo sauki ga rayuwar ma'aikata da ma talakan jihar, kama daga karin albashi da biyan hakkoki.
Kwamared Dabuwa ya ce ko a azumin Ramadan da aka kammala, al'ummar Jigawa sun yabawa gwamnan na kaddamar da shirin ciyar da talakawa da marasa galihu.
An kara wa ma'aikata albashi a Jigawa
A wani labarin, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Jigawa ta yi karin albashi na Naira 30,000 ga ma'aikatan jihar wanda zai yi aiki na watanni uku.
A cewar gwamnatin jihar, an yi karin albashin ne domin rage wa ma'aikatan radadin tsadar rayuwa da kasar ke fuskanta sakamakon janye tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng