Yayin da Ya Fara Fitar da Mai, Dangote Ya Samo Mafita Kan Tsadar Kayayyaki a Najeriya
- Shahararren attajiri a Najeriya, Aliko Dangote ya bayyana hanyar da za a saukar da farashin kayayyaki a Najeriya a nan gaba
- Dangote ya ce faduwar farashin bakin mai ne kadai zai saukar da farashin kayayyaki da ke dagula lamura a kasar
- Legit Hausa ta tattauna da malami kuma masanin tattalin arziki kan faduwar farashin kaya a Najeriya
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Legas – Yayin da ake fama da hauhawan farashin kaya, Alhaji Aliko Dangote ya kawo mafita domin fita daga wannan kangin.
Dangote ya ce dole sai farashin bakin mai ya sauka kafin a rabu da tsadar rayuwa da ake fama da ita a kasar, cewar ThisDay.
Nawa Dangote ke siyar da mai a matatarsa?
Attajirin ya bayyana haka ne a jiya Laraba 10 ga watan Afrilu a jihar Legas yayin da ya kai ziyarar gaisuwar sallah ga Shugaba Bola Tinubu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ce‘yan Najeriya su yi tsammanin raguwar farashin kaya idan farashin mai ya sauka da kaso biyu cikin uku.
Dan kasuwar ya ce matatarsa ta na siyar da mai din kan N1,200 kowace lita idan aka kwatanta da N1,700 a baya.
“A matatarmu, muna siyar da litar bakin mai kan N1,200 wanda a gaba na san hakan zai taimaka wurin rage hauhawan farashin kaya.”
- Aliko Dangote
Tabbacin Dangote kan farfadowar tattalin arziki
Dangote ya bayyana cewa ya na da tabbacin tattalin arzikin Najeriya zai farfado ganin yadda farashin naira ke tashi, cewar Arise News.
Ya ce yadda naira ke kara daraja daga N1,900 zuwa N1,250 har N1,300 hakan alama ce ta ana samun ci gaba a bangaren.
“Ina da tabbacin muna kan hanya madaidaiciya, ‘yan Najeriya suna da hakuri kuma za a fita daga wannan kangi.”
“Watakila zuwa gaba duk da danyen mai na kara tashi amma zai yi wahala mutane su sayi litar fiye da N1,200 wanda hakan zai saukar da farashin kaya.”
- Aliko Dangote
Iya faduwar bakin mai ba zai rage ba
Legit Hausa ta tattauna da malami kuma masanin tattalin arziki kan faduwar farashin kaya a Najeriya
Lamido Bello ya ce tabbas faduwar litar bakin mai zai rage farashin kaya amma ba iya shi kaɗai ake bukata ba.
"Tabbas zai yi tasiri amma fa dole sai an samu naira ta kara daraja wanda shi ne hanya mafi sauki."
"Watakila idan man fetur ne zai fi tasiri fiye da bakin mai ganin yadda aka fi amfani da fetur a kasar."
- Lamido Bello
Dangote ya fara siyar da mai
Kun ji cewa Matatar man Aliko Dangote ta fara siyar da mai a ranar Talata 2 ga watan Afrilu ga 'yan kasuwa.
Matatar ta shirya fitar da ganguna 650,000 a kowace rana inda ta gindaya sharuda ga 'yan kasuwar mai a Najeriya.
Asali: Legit.ng