Wuraren Shakatawa 5 da Ya Kamata Ku Ziyarta Yayin Bukukuwan Sallah a Kaduna
A jiya Laraba, al'umar Musulmi a fadin duniya suka yi sallar Idi karama, bayan kammala azumin Ramadan. Yanzu kuma, lokaci ne na yawon bude ido da shakatawa domin murnar Sallah.
Ga waɗanda suke a cikin jihar Kaduna, garin gwamna, ko kuma baki da suka ziyarci jihar a wannan lokaci na hutun Sallah, akwai bukatar ku fita ku shaka da kallon ababen ɗebe kewa.
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Akwai wuraren shakatawa da bude ido a Kaduna, wasu ma za ku iya ziyartarsu da 'yayanku, domin su yi wasanni.
Legit Hausa ta tattara bayani kan manyan wurare biyar na shakatawa a jihar Kaduna, kamar yadda jaridar Vanguard ta ruwaito.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
1. Gamji Park
Daya daga cikin al’adun Sallah a Kaduna shi ne taron ‘yan uwa da abokan arziki a filin wasanni na Gamji da ke tsakiyar babban birnin jihar.
Wannan wurin shakatawa wanda ya shahara saboda faffadan yanayinsa mai kyan gani, ya zama wuri mai dausayi ga masu shagalin biki da ke neman yin taro da daukar hotuna a cikin nishaɗi.
A filin wasanni na Gamji, masoya suna taruwa don yin raha, musayar kyaututtuka, da cin abinci na gargajiya.
2. Fadar sarki
Wani abin burgewa a shagulgulan Sallah da aka yi a Kaduna shi ne gagarumin bikin hawan Daba da ake gudanarwa a fadar SarkinZazzau, da ke Zariya.
Wannan bikin tsohuwar al'adar wanda ke tara dubunnan jama'a da ke zuwa daga ko'ina, yana nuna arziƙin al'adun yankin ta hanyar baje koli na hawan dowakai a yanayin shiga ta gargajiya.
Yayin da sautin kofaton dawakai ya cika iska, masu kallo kan tuna zamanin mutanen dauri, da irin jarumtar da sadaukai suka nuna a masarautar Zazzau, kamar dai Sarauniya Amina.
3. Dakin tarihi na kasa
Ga waɗanda suke son sanin tarihi da kuma kallon kayayyakin gargajiya na mutanen dauri, akwai bukatar su ziyarci dakin tarihi na kasa da ke Unguwan Sarki Kaduna.
Ga bakin da suka ziyarci dakin, ana nuna masu dukkanin kayayyakin al'adu na shekaru aru-aru da suka gabata, kama daga sutura, kwanukan abinci, kayan yaki, da sauransu, Wikipedia ta rahoto.
Hakazalika, za aji tarihin sarakunan masarautar Zazzau, da irin mulkin da suka shimfida da hotunan su, duk domin mutane su ilimantu a lokacin da kuma suke nishadi.
4/5. Gidan Arewa da Filin wasa na Murtala
Manyan wuraren shakatawa irin su gidan Arewa da filin wasanni na Murtala, wurare ne da ya kamata ku ziyarta yayin bukukuwan Sallah a Kaduna.
A wadannan wurare, za ka tarar da mutane kowa na nishadi, iyali sun taru, saurayi da budurwa, miji da mata, kowa yana harkokin gabansa.
Daga kidan taushi da ke tashi, zuwa raye-raye na al'ada, wadannan wuraren kan iya zama wajen da za ku iya samun nishadi a wannan sallar.
Sallar bana ba ta yi armashi ba?
Wasu 'yan Kaduna da Legit Hausa ta samu damar zantawa da su a ranar Sallah sun koka kan yadda aka yi sallar bana cikin rashin kudi da tsadar rayuwa.
Wani matashi, Umar da ke Makarfi Road, Rigasa Kaduna ya ce:
"Wannan sallar haka nayi ta ba dinki babu sabon takalmi, na manta rabon da na yi irin hakan. Gaskiya ba wani boye-boye muna karbar kebura a mulkin nan."
Muhammad Bello daga Makarfi Road, ya ce tsadar rayuwa ta sa wannan sallar ba a jin kamshin soyen kaji ko nama a gidan mutane, yana mai cewa:
"A bayan tun ana gobe Sallah za ka rika jiyo kamshin nama ko na cincin amma wannan sallar kamas ne alaji. Amma dai alhamdulillah tunda muna da rai da lafiya."
Tinubu ya raba abinci ga talaka
A wani labarin, shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu ya raba abinci ga talakawan Nijeriya domin rage radadin tsadar rayuwa.
Ministan yaɗa labarai, Mohammed Idris ne ya sanar da hakan a Sokoto yayin bikin raba ton 42,000 na hatsi da gwamnatin tarayya ta yi ga jihohi.
Asali: Legit.ng