Wuraren shakatawa 5 da zaku iya kai iyalanku a cikin Najeriya
Kasancewa kowacce karshen shekara itace lokacin da mutane ke warewa domin hutawa da kuma ziyarar wuraren hutu, dalilin haka wasu magidanta na neman shawarar iyalansu domin su tayasu zaben wuraren da suka dace suje domin su huta.
Ko da yake wasu na hutawa ne a gidajensu basa fita, wasu kuma na na neman shawarar iyalansu da abokan arziki domin bincike akan wurin da ya cancanta su je su huta, wasu kuma na yin balaguro zuwa kauyukansu, Kowacce hanya dai mutum ya zaba domin ya huta idan ta kwantamasa a zuciya tayi.
1. Ikogosi Resort a jihar Ekiti: Kaman dabbobi da tabki da kuma rafi Wanda ya samo asali daga ruwan dutse, yana jahar Ekiti ne. Yana kayatarwa kuma sosai ga masu yawon bude ido
2. ERIN IJESHA WATERFALL : idan kai mai yawan sha'awan abubuwan gargajiya ne, To erin ijesha wata magudaniyar ruwa ce da ake kiranta Olumirin wanda tana ijesha ne a jahar Osun, wani ruwane me gudana daga tsibiri zuwa wani dan karamin tabki.
DUBA WANNAN: Rahoto kan kisan kare dangi da ake yi wa musulman Rohingya a Burma
3. Yankari Game Reserve: Wannan ma wurin shakatawa ne mai saukin kudi a jihar Bauchi, wanda ke da wuraren bacci da wuraren yawo a cikin daji, wuraren linkaya a Wikki Spring, ruwa mai dumi daga cikin kasa, sannan dabbobi masu kayatarwa na dawa.
4. Obudu Ranch: Wannan ma wuri ne a can jihar Cross Ribas, inda mutane kan sami shakatawa da yawo a daji da hutu, in kana wurin kamar ba a kasar nan kake ba.
5. Tinapa a jihar Kalaba shima wuri ne da ke da wuraren hutawa da shakatawa wanda zai baiwa iyali hutub da suke samu a kasashen waje, cike yake da kasuwanni da wuraren zagawa da wasanni domin yara.
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/naijcomhausa
Twitter: https://twitter.com/naijcomhausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng