Sojoji Sun Cafke Hatsabibin Ɗan Ta'adda da Ya Yi Ajalin Janar Din Soja da Wasu Sojoji 3
- Rundunar sojoji a Najeriya ta sake yin nasara inda ta cafke kasurgumin dan ta'adda da ake nema ruwa a jallo a jihar Adamawa
- Dakarun sun cafke Saidu Hassan Yellow ne a kasuwar Mubi da ke jihar Adamawa a ranar 9 ga watan Afrilu na wannan shekara
- Ana zargin Yellow mai shekaru 32 da kitsa harin ne wanda ya yi ajalin janar din sojan da wasu guda 3 a garin Askira da ke Borno
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Adamawa - Rundunar sojoji ta yi nasarar cafke hatsabibin ɗan ta'adda da ya hallaka janar din sojan da wasu sojoji uku a jihar Borno.
Wanda ake zargin, Saidu Hassan Yellow da ya hallaka sojojin a Askira-Uba ya shiga hannun ne bayan rundunar ta kai samame.
Yaushe sojoji suka cafke ɗan ta'addan?
Dakarun "Operation Hadin Kai" da ke Madagali a jihar Adamawa sun samu nasarar cafke shi ne bayan samun bayanan sirri daga al'umma.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Kasurgumin ɗan ta'addan wanda rundunar ke nema ruwa a jallo ya shiga hannun jami'an sojojin ne a kasuwar Mubi a ranar 9 ga watan Afrilu.
Zagazola Makama ta tattaro cewa Yellow mai shekaru 32 ya kitsa harin ne a garin Askira a ranar 12 ga watan Nuwambar 2021.
Kayayyakin da aka samu a gun ɗan ta'addan
Daga cikin kayayyakin da aka samu a wurinsa akwai wayoyi guda 3 da katin cire kudi 3 da agogon hannu.
Sauran kayan da aka samu sun hada da zobe guda hudu da tulin makullin kofa da kuma N1900 kacal a jikinsa, cewar National Accord.
Rundunar ta sanar da cewa tuni ta tura ɗan ta'addan babban ofishin rundunar domin tabbatar da binciken kwa-kwaf.
Kasurgumin ɗan bindiga, Dangote ya mutu
A baya, mun kawo muku labarin cewa, kasurgumin ɗan bindiga da ya addabi jihar Zamfara, Sani Dangote ya mutu.
Dangote ya rasa ransa ne yayin artabu da abokan gaba karkashin jagorancin Kachalla Dankarami kan zargin satar shanu.
Matsalar da ke tsakaninsu ta jawo matsanancin fada wanda har ya yi ajalin Dangote da wasu 'yan uwansa guda 2.
Asali: Legit.ng