Bikin Sallah: Wurare 5 Masu Kayatarwa da Ya Kamata Ku Ziyarta a Kaduna
- An bankado wuraren shakatawa da al'ummar Musulmi yayin da ake hidimar kamar Salla a fadin Najeriya
- Wuraren sun hada da Arewa House wanda asali gida ne na Sardaunan Sokoto kafin a mayar da shi cibiyar Arewa
- Ana sa ran duk wanda ya halarci wadannan wuraren zai yi bikin sallah cikin nishadi tare da kara samun ilimin tarihi
Editan Legit Hausa Ibrahim Yusuf yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru hudu, kuma kwararre ne a kawo rahotannin kasuwanci, siyasa da lamuran yau da kullum.
Lokacin bikin sallah lokaci ne dake cike da nishadi, farin ciki da shagali.
Saboda haka ne mutane daban-daban suke ziyartar wurare masu kayatarwa da tarihi domin samun nishadi da ilimi.
A tarayyar Najeriya, ana gudanar da bukukuwan gargajiya da ziyarce-ziyarce a lokutan Sallah domin samun nishadi da kuma raya al'adu.
Innalillahi: Tsohon dan majalisar wakilai ya yanki jiki ya fadi bayan dawowa daga sallar idi a Abuja
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Amma jihar Kaduna, kasancewar ta tushe ne ga Arewa, ta kunshi wuraren tarihi masu kayatarwa wanda kowa zai so zuwa domin bawa idanunsa abinci.
A wani rahoto da jaridar Vanguard tayi, an gano wurare biyar masu kayatarwa a jihar Kaduna wanda kowa ya kamata ya kai ziyara domin more bikin sallah yadda ya kamata.
1. Gamji Park
Daya daga cikin al’adun Sallah a Kaduna shi ne taron ‘yan uwa da abokan arziki a Gamji Park da ke tsakiyar birnin jihar.
Wannan wurin shakatawa mai banƙaye, wanda ya shahara saboda faffadan yanayinsa mai kyan gani, kuma ya kasance wuri ne mai dausayi.
Gamji Park wuri ne mai cike da ciyawa mai laushi, masoya suna taruwa domin yin dariya, raha, ba da kyauta dama cin abincin gargajiya.
2. Fadar sarki
Wani abin burgewa a shagulgulan Sallah da ake yi a Kaduna shi ne hawan daba da ake gudanarwa a fadar Sarkin Zariya.
Taro ne da ke tara jama'a daga nesa da ko'ina, wannan tsohuwar al'adar tana nuna al'adun mutanen Arewa ta hanyar baje kolin hawan dawakai.
3. Gidan kayan tarihi na kasa
Ga masu neman samun ilimin tarihi da al’adu, gidan tarihi na kasa da ke Unguwan Sarki Kaduna wuri ne dake cike da kayan tarihi masu jan hankali.
Ana bawa baƙi damar ɗaukar taska na tsoffin kayan tarihi, Kayan tarihin suna ilmantar wa game da al'adu, da nuna wayewar zamanin irinta shekarun baya.
4. Arewa House da Murtala Square
Manyan wuraren tarihi irin su Arewa House da Dandalin Murtala suma suna ba da damammaki na nishadantarwa da sharholiya.
A wadannan wurare masu ban sha'awa, ana samun masu fasaha da masu yin wasan kwaikwayo da ke nishadantar da masu sauraro.
Wadannan sune jerin wurare 5 masu banƙaye a jihar Kaduna, amma kamar yadda Bahaushe yake cewa gani ya kori ji, to duk wanda yaje zai ba da labari.
Arewa House ya cika shekara hamsin
A wajen bikin cika shekaru 50 da kafa Arewa House da ke Kaduna, Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya karrama mutumin da ya tuka, Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello.
An ruwaito cewa gwamnonin jihohin Ekiti, Jigawa, Kebbi da Kaduna sun kasance daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron.
Asali: Legit.ng