Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Faɗi a Arewa House Ya Janyo Maganganu

- Wani bidiyo da ke nuna lokacin da Bola Ahmed Tinubu ya yanke jiki ya fadi ya janyo cece-kuce tsakanin yan Nigeria

- Jagoran na kasa na jam'iyyar APC ya fadi ne a wurin taron shekara-shekara karo na 11 na Arewa House da ake yi a Kaduna shekarar 2021

- Wasu sun ce tsautsayi ne da zai iya faruwa da kowa yayin da wasu kuma suke ganin wani abu da ya dace a zurfafa bincike

Wani faifan bidiyo da ya fito da ke nuna jagoran jam'iyyar All Progressives Congress, APC, na kasa ya yi yanke jiki ya fadi ya janyo maganganu tsakanin yan Nigeria.

Tsohon gwamnan na jihar Legas, Bola Ahmed Tinubu ya yanke jiki ya fadi yayin taron Arewa House karo na 11 da aka yi a dakin taro na Banquet da ke Kaduna.

Kara karanta wannan

Tallafi Na Jiransa: Dan Najeriya Ya Sa A Nemo Masa Mubarak Yusuf, Yaro Makanike Da Ke Zuba Turanci A Bidiyo

DUBA WANNAN: Na Bar Mijina Saboda Girman Mazakutarsa, Matar Aure ta Shaidawa Kotu

Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Arewa House Ya Janyo Maganganu
Bidiyon Tinubu Ya Yanke Jiki Ya Fadi a Arewa House Ya Janyo Maganganu. @emmaikumeh
Asali: Twitter

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

A bidiyon da wani mai amfani da Twitter @emmaikumeh ya wallafa, Tinubu, wanda shine shugaban taron ya yanke jiki ya fadi yayin da ya ke kokarin tafiya tsakanin wasu kujeru da masu tsaronsa a tare da shi.

KU KARANTA: EFCC ta Kama Mahaifiya da Ɗanta kan Damfara ta Intanet a Legas

Ba a tabbatar da abinda ya yi sanadin faduwarsa ba amma nan take masu tsaronsa sun taimaka sun daga shi da suka gano abinda ke faruwa.

Ga bidiyon a nan kasa:

Bidiyon ya janyo cece-kuce tsakanin yan Nigeria a Twitter.

Wasu na cewa wannan ba wani abu bane domin zai iya faruwa da kowa yayin da wasu ke ganin kamar alama ce da ke nuna ba shi da lafiya kuma ya kamata a duba batun musamman saboda hasashen da ake yi na cewa zai yi takarar shugaban kasa a 2023.

Kara karanta wannan

Tsohon shugaba Goodluck ne alherin da Najeriya ta taba gani a tarihi, inji gwamnan Arewa

@PreciousAmurika ta ce:

"Mutumin da ke fadi kamar tsohuwar fanka na tsaye yana son ya zama shugaban kasa tamkar mataccen katakon da muke da shi a yau."

@macfriet ta ce

"Ina ganin kawai ya taka babban rigarsa ne yayin da ya ke tafiya, kada ku yi saurin yanke hukuncin, Idan da fadi ya yi bai tashi ba, da an garzaya da shi asibiti. Amma ya tsaya ya gabatar da kasidarsa."

@uchebakaadi ya ce:

"Akwai yiwuwar Alhaji ya yi karo da wani abu a wurin taron nan. Wancan ranar hannunsa na rawar kamar DJ Jimmy Jatt a wurin taro. Watakila lokaci ya yi da zai yi murabus ya koma gida ya huta da yaransa da matarsa. Akwai yiwuwar Asiwaju bai fadi ba. Allah ba zai kunyata mu ba."

A wani rahoton daban, kun ji cewa Jami'an Hukumar Hisabah ta jihar Kano sun gargadi daliban Jami'ar Bayero da ke Kano wadanda ke zaune a gidajen da ke wajen makaranta su kauracewa aikata ayyukan masha'a, Vanguard ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Kano: Gini Mai Hawa Ɗaya Ya Rufta Wa Yara 3 Yan Gida Daya, Biyu Cikinsu Sun Mutu

Hakan na zuwa ne bayan kama wasu dalibai mace da namiji a cikin daki guda a wani gida kwanan dalibai da ke kusa da kusa da jami'ar.

Jami'an na Hisbah sun kuma ce za a ci tarar N20,000 ga duk wani dalibi namiji da mace da aka kama su a daki guda kamar yadda majiyoyi suka shaidawa SaharaReporters

Asali: Legit.ng

Tags:
Online view pixel