Bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa: An karrama direban Sardauna

Bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa: An karrama direban Sardauna

- Sarkin Musulmi, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya karrama direban Sir Ahmadu Bello

- Har ila yau Sultan ya bukaci manyan bakin wajen da su karrama direban mai suna Alhaji Ali Sarkin Mota

- Hakan dai ya kasance ne a wajen taron bikin shekaru hamsin da kafa Arewa House da ke Kaduna

A wajen bikin cika shekaru 50 da kafa Arewa House da ke Kaduna, Sultan na Sokoto, Alhaji Muhammad Sa’ad Abubakar, ya karrama mutumin da ya tuka, Firimiyan Arewacin Najeriya, Sir Ahmadu Bello.

Sultan ya bukaci manyan baki da masu ruwa da tsaki da suka halarci taron da su karrama Alhaji Ali Sarkin Mota, sannan dattijon ya dunga bin wuri-wuri a dakin taron domin gaisawa da manyan mutane da taimakon sandar da yake dogarawa.

KU KARANTA KUMA: Sheikh Sudais ya yi Allah-wadai da masu yin batanci ga Annabi

Bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa: An karrama direban Sardauna
Bikin shekara 50 da kafa Gidan Arewa: An karrama direban Sardauna Hoto: @daily_trust
Asali: Twitter

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa gwamnonin jihohin Ekiti, Jigawa, Kebbi da Kaduna sun kasance daga cikin manyan mutanen da suka halarci taron.

KU KARANTA KUMA: Yadda wata mota ta kutsa kai cikin Masallacin Ka’aba da gudu

Sauran manyan bakin sun hada da tsohon Mataimakin Shugaban Kasa, Muhammada Namadi Sambo, Ministan Muhalli, Mohammed Mahmud Abubakar ta takwaransa na Ma’aikatar Harkokin ‘Yan Sanda, Maigari Dingyadi da sauransu.

Gwamnan Jihar Ekiti kuma Shugaban Kungiyar Gwamnonin Najeriya, Kayode Fayemi shi ne babban bako mai jawabi a wurin taron.

A wani labarin, 'Yar gwagwarmaya, Aisha Yesufu, ta yi shagube ga Musulman da suka dinga caccakarta saboda 'ta yi uwa, ta yi makarbiya' a zanga-zangar ENDSARS.

Aisha, wacce sunanta ya kara karada gari saboda zanga-zangar ENDSARS, ta ce ko kadan hakan bai taba damunta ba.

"Na ji cewa na sha tsinuwa a Masallatai, mutane suna zama domin kawai su tsinemin bayan sun idar da Sallah.

"Tambayata wurinsu guda daya ce; sau nawa suka yi min irin wannan tsinuwar a lokacin da nake caccakar tsohon shugaban kasa Jonathan! Dukkanmu tsinannu a Najeriya," in ji ta

Domin sauke manhajar labaran Legit.ng a wayar ku ta hannu, latsa wannan rubutu na kasa: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng