Shirye-Shiryen Bikin Sallah, Gwamnan Jihar Arewa Ya Jibge Jami’an Tsaro

Shirye-Shiryen Bikin Sallah, Gwamnan Jihar Arewa Ya Jibge Jami’an Tsaro

  • Gwamnatin jihar Yobe ta ce ta jibge jami'an tsaro a lungu da sakuna na jihar domin tabbatar da tsaro a lokutan bikin Sallah karama
  • Gwamnan jihar, Mai Mala Buni ya sanar da hakan a yayin gudanar da wani taro na majalisar tsaro tare da shugabannin tsaro na jihar
  • Shi ma kwamishinan 'yan sandan jihar Yobe, Ahmad Garba, ya fadi irin matakan da rundunar ta dauka na tabbatar da tsaron al'umma

Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida

Jihar Yobe - Gwamnatin jihar Yobe ta bayar da tabbacin cewa ta kammala dukkanin shirye-shirye domin ganin an gudanar da bukukuwan Sallah-El-Fitr cikin kwanciyar hankali a jihar.

Gwamnan Yobe ya dauki matakan tsaro a shirin bikin Sallah
Gwamna Mai Mala Buni ya ce an jibge jami'an tsaro a wuraren taruwar jama'a. Hoto: @MalaBuni
Asali: Twitter

Gwamna Mai Mala Buni ya bayar da wannan tabbacin a wani muhimmin taron majalisar tsaro da shugabannin hukumomin tsaro na jihar suka gudanar.

Kara karanta wannan

Karamar Sallah 2024: Gwamnatin Kano ta tallafawa mazauna gidan gyaran hali da abinci da shanu

An jibge jami'an tsaro a Yobe

Mataimakin gwamnan jihar, Hon Idi Gubana ne ya wakilci Buni a taron, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Gwamna Buni ya ce an jibge jami’an tsaro domin kula da muhimman wurare da ake da tabbacin jama'a za su taru domin tabbatar da zaman lafiya.

Ya kara da cewa an sanar da jami’an tsaro da su kasance a wurare masu muhimmanci kafin bikin, da kuma bayan bikin, domin dakile duk wata barazana ta tsaro.

Matakan tsaro a bangaren 'yan sanda

A martaninsa bayan taron, kwamishinan ‘yan sandan jihar, Ahmad Garba ya ce matakan tsaron da aka dauka sun hada da tura jami’an tsaro a harabar idi a fadin jihar.

Garba ya ci gaba da cewa idan har aka samar da tsaro, kowa zai yi farin ciki tare da yin hutun Sallah cikin kwanciyar hankali.

Kara karanta wannan

Ruwan sama ya lalata gine-gine tare da raba mutane 3,000 da gidajensu a Kogi

Kwamishinan ‘yan sandan ya bukaci iyaye da masu kula da yara da su sanya ido kan motsin ‘ya’yansu da kai rahoton ba-ta-gari a yayin bukukuwan Sallah.

NSCDC ta jigbe jami'ai 862

Jaridar Daily Trust ta ruwaito cewa hukumar tsaron farar hula (NSCDC) ta jihar Yobe, ta ce ta jibge akalla jami'anta 862 a fadin jihar yayin bikin sallar.

Bala Garba, jami'in hulda da jama'a na hukumar ne ya bayyana hakan ga manema labarai a Damaturu, babban birnin jihar.

"Za a yi rana a ranakun Sallah" - NiMET

Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa hukumar da ke kula da yanayi ta kasa (NiMET) ta sanar da cewa za a yi zafin rana a kwanakin bikin Sallah.

Hasashen yanayi da hukumar ta fitar a ranar Litinin ya nuna cewa za a yi rana sosai a ranakun Talata har zuwa Alhamis, da kuma tsawa a wasu jihohin Arewa.

Asali: Legit.ng

Authors:
Sani Hamza avatar

Sani Hamza Sani Hamza ma'aikaci ne da ya yake da gogewa a aikin jarida. Ba fassara labarai da wallafasu a yanar gizo kadai ba, Sani yana da kwarewa a aikin rediyo da talabijin. Ya kuma shafe shekaru 8 a masana'antar fina-finai da dab'i.