Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge ’Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano

Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge ’Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano

- Rundunar 'yan sanda a jihar Kano ta jibge jami'anta sama da 4000 a fadin jihar don tabbatar da tsaro

- Rundunar ta bayyana wasu shawarwari da ya kamata iyaye da sauran masu zuwa sallahr Idi su kiyaye

- Hakazalika rundunar ta fara kai samame maboyar bata-gari don tabbatar da an yi bikin sallah laifya

Rundunar ‘yan sanda a jihar Kano ta tura jami’anta 4,144 don samar da tsaro a fadin jihar yayin bukukuwan Sallah.

Hakan na kunshe ne cikin wata sanarwa da kakakin rundunar, ASP Abdullahi Haruna ya fitar a ranar Laraba a Kano.

Haruna ya ce za a tura ‘yan sanda zuwa wurare masu mahimmanci da suka hada da filayen Sallar Idi a lokacin bikin, Daily Nigerian ta ruwaito.

Kakakin ya ce rundunar tana aiki tare da sauran hukumomin tsaro da na sa kai cikin farar hula don tabbatar da kariya ga rayuka da dukiyoyi.

KU KARANTA: Jerin Kasashen Da Basu Ga Wata Ba, Ba Kuma Za Su Yi Sallar Idi Gobe Laraba Ba

Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge 'Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano
Tabbatar da Tsaro a Bikin Sallah: An Jibge 'Yan Sanda Sama da 4000 a Jihar Kano Hoto: punchng.com
Asali: UGC

“Rundunar tana shawartar mazauna jihar da su yi taka tsan-tsan tare da kiyaye shawarwarin tsaro.

“Ana shawartar masu bauta da za su je filin Sallar Idi da su guji daukar wasu abubuwa marasa amfani wadanda za su iya haifar da zargi ko fargaba.

“Yara masu kananan shekaru da kuma wadanda ba su da lasisi ba su da izinin yin amfani da motoci, babura masu kafa uku, sauran babura da kekuna yayin zuwa filin sallar Idi.

Ya ce "Iyaye su kasance tare da yaransu ko su hada yaran da manya yayin da za su je filin Sallar domin duba lamarin yaran da suka bata, hadari ko duk wata mu'amala da ba a so," in ji shi.

Mista Abdullahi ya yi kira ga kungiyoyi da daidaikun mutane da su guji aikata duk wani abin da zai kawo cikas ga zaman lafiya, yana mai gargadin cewa za a kama wadanda suka saba doka kuma a hukunta su.

Ya kuma bukaci mazauna yankin da su kiyaye ka'idojin Korona, gami da sanya takunkumin fuska da kiyaye tazara tsakanin jama'a a duk lokacin bikin.

A cewarsa, rundunar ta fara gudanar da sintiri mai tsauri tare da kai samame maboyar masu aikata laifuka don kauce wa keta zaman lafiya daga masu aikata laifi da bata gari a jihar.

KU KARANTA: Bukukuwan Sallah: Abubuwa 9 da Musulmi Ya Kamata Ya Yi Kafin Sallar Idi

A wani labarin, Rundunar ‘yan sanda reshen jihar Imo a ranar Talata ta ce ta tura jimillar jami’anta 3200 don tabbatar da isasshen tsaro a jihar yayin da musulmai muminai ke bikin karamar Sallah, Channels Tv ta ruwaito.

A wata sanarwa da aka ba manema labarai dauke da sa hannun jami’in hulda da jama’a na ‘yan sanda, Orlando Ikeokwu, rundunar ta tabbatar wa al'ummar Imo cewa tana hada kai da dukkan hukumomin tsaro a jihar.

Ikeokwu ya ce ‘yan sanda sun yi shiri yadda ya kamata don tabbatar da tsaron rayuka da dukiyoyi a lokacin bikin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.