Yau take Sallah: Jami’an tsaro sun bazama a garin Kano don tabbatar da tsaro
Rundunar Yansandan jahar Kano ta sanar da cewa ta zuba wadataccen adadin jami’anta a cikin garin Kano domin tabbatar da ganin an gudanar da shagulgulan karamar Sallah cikin lumana, zaman lafiya da kwanciyar hankali.
Legit.ng ta ruwaito kaakakin rundunar, DSP Abdullahi Haruna ne ya bayyana haka yayin da yake ganawa da manema labaru a ranar Litinin, 3 ga watan Yuni a babban ofishin rundunar Yansandan jahar.
KU KARANTA; Almubazzarancin 3.4bn: Hukumar yaki da rashawa ta shawarci Ganduje ya dakatar da Sarki Sunusi II
A jawabinsa, kaakaki Haruna ya bayyana cewa baya ga jami’an Yansanda da zasu bada tsaro, rundunar ta hada kai da hukumar kare haddura ta kasa, FRSC, hukumar tsaron farin kaya, NSDC, hukumar kula da dokar hanya ta Kano, KAROTA, da hukumar Hisbah don tabbatar da zirga zirga ababen hawa cikin sauki.
“Mun tanadi tsare tsaren tsaro a filayen sallar Idi, don haka muke kira ga masallata da su guji daukan abinda basu bukata zuwa filin sallar Idi, musamman duk wani abu da zai kawo fargaba ko tsoratarwa ga jama’a.” Inji shi.
Haka zalika kaakakin ya nemi jama’a masu halartar wuraren wasanni da wuraren shakatawa a yayin shagulgulan sallah dasu tabbata sun kasance masu lura da duk wani abu dake wakana a inda suke don kare kansu da dukiyoyinsu daga miyagu.
Daga karshe kaakakin Yansandan yayi kira ga jama’a dasu baiwa hukumomin tsaro hadin kai wajen gudanar da aikinsu, ta yadda zasu samar da ingantaccen yanayi don gudanar bukukuwan sallah cikin nishadi.
Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa
ko a http://twitter.com/legitcomhausa
KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki
Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com
Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa
Asali: Legit.ng