Gwamnatin Najeriya za ta shuka itatuwa miliyan 30 a 2020

Gwamnatin Najeriya za ta shuka itatuwa miliyan 30 a 2020

- Gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin shuka itatuwa guda miliyan 30 a cikin wannan shekara ta 2020

- An tattaro cewa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ware wasu kudade domin shuka itatuwa miliyan 30

- Mataimakin shugaban sashen kula da dazuka na ma’aikatar muhalli Tiamiyu Oladele ne ya bayyana hakan

Rahotanni sun kawo cewa gwamnatin tarayyar Najeriya na shirin shuka itatuwa guda miliyan 30 a cikin wannan shekara ta 2020.

Mataimakin shugaban sashen kula da dazuka na ma’aikatar muhalli Tiamiyu Oladele ne ya bayyana hakan a wata hira da kamfanin dillancin labaran Najeriya a ranar Litinin, 17 ga watan Fabrairu.

A cewarsa shugaban kasa Muhammadu Buhari ya yi alkawarin ware wasu kudade domin shuka itatuwa miliyan 30 inda ya ce ma’aikatar muhalli ta kammala shiri tsaf domin ganin haka ya tabbata.

Gwamnatin Najeriya za ta shuka itatuwa miliyan 30 a 2020
Gwamnatin Najeriya za ta shuka itatuwa miliyan 30 a 2020
Asali: UGC

“Ma’aikatar mu ta shirya ta shuka itatuwa miliyan 30 daga cikin miliyan 35 a cikin wannan shekara sannan ma’aikatar za ta raba irin itatuwan ga manoma da mutane domin shukawa a gonaki da wurare mafi kusa."

Ya ce ‘yan katako da masu yin gawayi na cikin mutanen dake sare itatuwa ba tare da suna shuka wani ba.

KU KARANTA KUMA: Tashin hankali: Yan bindiga sun kashe sojoji 4 da yan farar hula 2 a Bayelsa

“Gwamnati zata ci gaba da wayar da kan mutane sanin illar dake tattare da sare itatuwa ga muhalli da amfanin da barin shi ke yi wa kiwon lafiyar mutane.

“Za kuma a kafa kwamiti wanda a ciki akwai wakilan ma’aikatan muhalli, ‘Yan katako da masu yin gawayi wanda za su sa ido wajen ganin an hana mutane sare itatuwa ba tare da izini ba,” in ji shi.

A wani labarin kuma, mun ji cewa majalisar wakilai ta yi odan motocin alfarma guda 400 kirar Toyota Camry 2020 domin amfanin yan majalisar su 360, kamar yadda shuwagabannin majalisar suka yanke hukunci a wani taro da suka yi a ranar 5 ga watan Feburairu.

Jaridar Punch ta ruwaito wata majiya da ta nemi a sakaya sunanta ta tabbatar da amincewar majalisar na sayo motocin alarma guda 400, sai bata bayyana farashin da majalisar za ta sayo motocin a kai ba.

Idan ku na da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewa tare da mu.

Asali: Legit.ng

Authors:
Aisha Musa avatar

Aisha Musa (Hausa writer) Aisha Musa 'yar jarida ce wacce ta kwashe shekaru biyar tana aikin gogewa a harkar yada labarai. Ta kammala karatun ta a Jami'ar Ibrahim Badamasi Babangida (IBB Lapai) a shekarar 2014 tare da digirin farko a fannin Tarihi. Aisha Editan Hausa ce wacce ke amfani da kwarewa da kwazonta don karfafawa wasu gwiwar yin aiki tukuru don cimma nasara. Ta karbi lambar yabo na gwarzuwar shekarar 2021 a bangaren Hausa na Legit. Za ku iya aika mata sakonnin imel ta adireshinta aisha.musa@corp.legit.ng