"N550 Duk Lita": 'Yan Kasuwa Sun Yi Magana Kan Farashin Man Fetur a Matatar Man Dangote
- Ƴan kasuwar man fetur a Najeriya sun kawo sabon farashin mai a daidai lokacin da matatar man Dangote ke shirin fara sayar da shi a kasuwa
- Rahotanni sun bayyana cewa ƴan kasuwar sun bada shawarar sanya sabon farashin Naira 550 kan kowace lita ga matatar man fetur ɗin
- Wannan mataki dai ya faru ne saboda kamfanin NNPC Limited na sayar da man fetur ga dillalan mai kan naira 556 kowacce lita, inda suke sayarwa ƴan kasuwa kan Naira 640
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Editan Legit Hausa Sharif Lawal yana da ƙwarewar shekaru wajen kawo rahotannin siyasa, al'amuran yau da kullum, tsegumi da nishaɗi
Jihar Legas - Matatar man fetur ta Dangote da ke a Legas, ta kusa fara shigo da mai cikin kasuwa.
Mahukuntan matatar man da ƴan kasuwa na ci gaba da tattaunawa kan farashin da za a sayar tare da aikawa da shi zuwa gidajen mai a faɗin ƙasar nan.
Ƴan kasuwa za su karya farashin fetur
Matatar man fetur ɗin wacce za ta iya tace gangunan mai 650,000 a kowace rana, ta shirya fara fitar da man fetur nan da watan Mayun 2024.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cewar rahotanni, ƴan kasuwar da mahukuntan matatar man sun tattauna kan farashin da ya kamata a sanyawa man fetur ɗin a kasuwa.
Masu wuraren ajiye man fetur suna sayowa daga NNPCL kan N556 kan kowace lita inda suke sayarwa ƴan kasuwa kan N640.
Jaridar Vanguard ta rahoto cewa ƴan kasuwar sun ba mahukuntan matatar man fetur ta Dangote shawarar sanya farashin Naira 550 kan kowace lita, yayin da suke ci gaba da tattaunawa.
Ƴan kasuwa na tattaunawa da matatar Dangote
Abubakar Migandi Garima, shugaban ƙungiyar ƴan kasuwar man fetur ta IPMAN, ya tabbatar da cewa suna tattaunawa da mahukuntan matatar kan farashin da sauran abubuwa.
Ya bayyana cewa abubuwa da dama na taka rawa wajen farashin man fetur ciki har da kuɗin da ake sayo shi da yadda ake gudanar da matatar man fetur ɗin.
Migandi ya bayyana cewa akwai yiwuwar farashin man fetur ya ragu a Najeriya lokacin da matatar man fetur ɗin za ta fara tace ganga 650,0000 kowace rana.
Fetur: Man Dangote ya shigo kasuwa
A wani labarin kuma, kun ji cewa matatar man Aliko Dangote ta fara sayar da mai a ranar Talata, 2 ga watan Afrilu ga ƴan kasuwa.
Matatar za ta riƙa sayar da litar man fetur miliyan ɗaya ga kowane ɗan kasuwa yayin da ta gindaya musu sababbin sharuɗɗa.
Asali: Legit.ng