“Za Mu Waiwayi Bidiyon Dala”: Abba Ya Magantu Kan Shekara 8 Na Mulkin Ganduje a Kano
- Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya ce watanni takwas da ya yi a mulki sun zarce shekaru takwas da Abdullahi Ganduje ya yi
- Yusuf ya ce babu komai a cikin gwamnatin Dr. Ganduje face cin hanci da rashawa da kuma karkatar da kadarorin gwamnatin Kano
- Gwamnan ya sha alwashin cewa zai sake gudanar da bincike kan bidoyon da aka nuna Ganduje yana karbar daloli daga 'yan kwangila
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Kano - A ranar Lahadi ne gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf, ya mayar da martani ga Abdullahi Umar Ganduje kan ikirarin cewa bai iya shugabanci ba.
Abba Yusuf ya ce shekaru takwas da Ganduje ya yi a mulkin jihar Kano bai tsinana wa al'uma komai ba sai ma cin zarafin ofis da yayi, kamar yadda jaridar Daily Trust ta ruwaito.
Ganduje ya kalubalanci mulkin Abba
Legit Hausa ta rahoto Ganduje, wanda a yanzu shi ne shugaban jam'iyyar APC na kasa, ya zargi Gwamna Yusuf da cewa ya gaza tafiyar da mulkin Kano yadda ya kamata.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A cikin wata sanarwa daga sakataren watsa labaransa, Edwin Olufu, Ganduje ya ce gwamnan na amfani da dabarar janye hankalin jama'a daga gane gazawarsa a fili.
Ya ce duk da irin maƙudan kudaden jihohi ke samu daga gwamnatin tarayya, babu wani aikin kirki da Abba ya yi a Kano, sai neman takalar rigima.
Ganduje na martani ne kan kwamitin da gwamnatin Kano ta kafa wanda zai bincike shi a kan zargin karkatar da kadarori da kuma rashawar $413,000 da N1.38bn.
Watanni 8 na mulkin Abba a Kano
Sai dai Gwamna Yusuf a wata sanarwa daga mai magana da yawunsa, Sanusi Bature Dawakin Tofa, ya ce babu komai a mulkin Tinubu sai cin hanci da rashawa da karkatar da kadarorin gwamnati.
Jaridar Vanguard ta ruwaito sanarwar ta ce:
"Watanni takwas na Gwamna Abba Kabir Yusuf sun zarce shekarau takwas da Ganduje ya bata a mulki na kama karya.
"Wannan gwamnatin ba za ta yi kasa a guiwa ba wajen ganin ta hukunta duk wanda aka kama da laifin karbar cin hanci da rashawa ko wanene shi."
Abba zai waiwai bidiyon 'Gandollar'
Hakazalika, sanarwar tace gwamnatin Abba ba za ta manta da bidoyon tsohon gwamnan da aka nuna yana karbar daloli ba, dole sai ta yi bincike a kai, jaridar Leadership ta ruwaito.
Gwamnan jihar ya kuma nemi da a bashi sakamakon binciken da aka yi kan bidoyon wanda hukumar EFCC ta aiwatar domin yin bincike a kai.
Abba ya kafa kwamitin binciken Ganduje
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa gwamnatin jihar Kano ta kafa kwamiti da zai binciki yadda Abdullahi Umar Ganduje ya tafiyar da mulkin Kano.
Hakazalika ta kafa kwamitin da zai binciki tashin hankalun da aka yi da satar yara da kashe mutane a zabukan jihar daga 2015 zuwa 2023.
Asali: Legit.ng