Gandollar: Hukumar yaki da rashin gaskiya ta yi bayanin abin da ya hana ta cafke Ganduje

Gandollar: Hukumar yaki da rashin gaskiya ta yi bayanin abin da ya hana ta cafke Ganduje

  • Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya yi magana game da bidiyoyin ‘Gandollars’
  • Ana zargin Gwamnan Kano da karbar cin hanci a hannun ‘yan kwangila
  • Hukumar yaki da rashin gaskiya ta fadi abin da ya tsaida binciken Gwamna

Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya ce bidiyoyin da ake zargin an ga gwamnan Kano, Abdullahi Umar Ganduje, ya na karbar cin hanci zai yi wahalar ayi aiki da su.

Jaridar Premium Times ta ce shugaban hukumar da ke yaki da rashin gaskiya ta jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin-Gado ya bayyana haka a ranar Asabar.

An shirya wani taro domin a auna yadda ake yaki da rashin gaskiya a Najeriya tsakann shekarar 2015 da 2020 a garin Legas inda Magaji Rimin-Gado ya yi magana.

KU KARANTA: Dalilin da ya sa aka daina bincike kan faifan dalolin Ganduje

A cewar Muhuyi Magaji Rimin-Gado, babu wadanda suka zo wajen hukumar domin su bada hadin-kai a kan yadda za a binciki gwamnan, a gurfanar da shi.

Lokacin da bidiyon da ake magana suka fara bayyana a kafar yanar gizo, an daura masu wakoki, dauke da karin bayanai, a cewar shugaban hukumar ta jihar Kano.

Ya ce: “Bayan wani da ya sakaya sunansa ya aiko mana takarda cewa ku binciki gwamnan, mun sanar da ‘yan jarida cewa akwai yadda ake bi wajen yin bincike.”

Magaji Rimin-Gado yake cewa da aka bibiyi masu neman a binciki gwamna, sai aka gano cewa dukkaninsu sun bada lambobin wayoyi da kuma adireshin bogi ne.

KU KARANTA: Ana binciken Sarkin Kano da Mukarrabansa a kan badakalar N1.3bn

Gandollar: Hukumar yaki da rashin gaskiya ta yi bayanin abin da ya hana ta cafke Ganduje
Abdullahi Umar Ganduje Hoto: premiumtimesng.com
Asali: UGC

“Akwai matakan da mu ke bi, ko da kuwa wanda ya kai korafi bai so ya bayyana a bainar jama’a.” Jaridar ta rahoto Rimin Gado ya na karin-haske a karshen mako.

“Bayan nan da aka gayyaci sunayen wasu da aka ambata a bidiyon, sai suka ki zuwa su yi bayani, suka barranta kansu daga bidiyon, ba za mu iya bincike a haka ba.”

Rimin Gado ya ce a yadda lamarin ya kasance, ba zai yiwu a binciki Dr. Abdullahi Ganduje ba domin ana bukatar a iya gabatar da hujjoji masu karfi a gaban kotu.

Kwanaki kun ji shugaban hukumar da ke sauraron korafin jama’a da binciken marasa gaskiya a jihar Kano, Muhuyi Magaji Rimin Gado, ya yi abinda ake ta yabonsa.

Rahotanni sun ce an yi wa Muhuyi Magaji Rimin Gado tayin miliyoyin kudi a matsayin cin hanci, domin ya dakatar da bincikenn badakalar masaratu, amma ya ki karba.

Asali: Legit.ng

Online view pixel