Yaki da Garkuwa da Mutane: ’Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 85 da Ake Zargin ’Yan Ta’adda Ne

Yaki da Garkuwa da Mutane: ’Yan Sanda Sun Yi Ram da Mutum 85 da Ake Zargin ’Yan Ta’adda Ne

  • 'Yan sanda sun yi nasarar kame wasu da ake zargi da aikata laifuka daban-daban a babban birnin tarayya Abuja
  • Ya zuwa yanzu, ana tantancewa don gano ainihin wadanda ke aikata laifukan, inda za a gurfanar dasu nan kusa
  • Rahoto ya bayyana irin kayayyakin da aka kwato daga hannunsu da kuma inda ake tunanin sun sato su

Salisu Ibrahim ne babban editan sashen Hausa na Legit. Kwararren marubucin fasaha, harkar kudi da al'amuran yau da kullum ne, yana da gogewar aikin jarida da rubuce-rubucen adabi sama da shekaru takwas

FCT, Abuja - A ci gaba da dakile yawautar satar mutane, jami’an 'yan sandan babban birnin tarayya Abuja sun yi nasarar kame wasu mutane 85 da ake zargi da aikata laifuka a birnin.

An kama mutanen ne a wani samame na hadin gwiwa tsakanin ranar 31 ga Maris zuwa 4 ga Afrilu, 2024, a lokacin da ‘yan sanda suka afkawa maboyar ‘yan ta’adda a Durumi da Dei-Dei a yankin Abuja.

Kara karanta wannan

Mafita mafi sauki: Reno Omokri ya ba 'yan Najeriya shawarin yadda za su shawo kan karyewar Naira

Rundunar ‘yan sandan ta ce wadanda ake zargin an kama su ne da laifuffuka daban-daban da suka hada da zama a haramtattun gine-gine da sayar da muggan kwayoyi da kuma kera kudaden jabu.

An kama 'yan ta'adda a Abuja
Yadda aka kame 'yan ta'adda a birnin Abuja | Hoto: NPF
Asali: Facebook

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Abubuwan da aka kwato daga hannun 'yan ta'addan

A wata sanarwa da jami’ar hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan babban birnin tarayya Abuja, SP Josephine Adeh ta fitar a ranar Lahadi, ta ce an aiwatar aikin samamen ne a gine-ginen da ke yankin, inda aka kwato kayayyakin barna a hannunsu, The Nation ta ruwaito.

A cewarta, an kwato janareta bakwai, wasu nau'ikan na'urori, da katunan ATM da dama da ake zargin sun sato su ne daga wadanda suka yiwa aikin ta'addanci.

Ta kuma kara da cewa, za a binciki wadanda aka kamen tare da gurfanar da masu laifi a kotun don daukar matakin da ya dace, kamar yadda jaridar Leadership ta ruwaito.

Kara karanta wannan

Adadin mutanen da aka kashe a harin Kogi ya karu, an roki Tinubu ya dauki mataki

Babban birnin tarayya na daga biranen da a Najeriya ke fuskantar matsalolin sace mutane da kuma barnata dukiyoyinsu.

An kame wadanda ake zargi da kashe 'yan sanda a Delta

A wani labarin, kun ji yadda 'yan sanda suka yi ram da wasu tsagerun da ake zargin suna da hannu a kisan jami'an tsaro a jihar Delta.

A makwannin da suka gabata ne rahotanni suka yi bayanin yadda wasu 'yan ta'adda suka yiwa jami'an 'yan sanda kwanton bauna a jihar.

Ya zuwa yanzu, ana ci gaba da bincike don kaiwa ga tushen yadda barnar ta faro da kuma yadda za a gurfanar da masu laifin.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.