Sojoji Na Nuna Wariya Wurin Fifita Sojojin Arewa Kan ’Yan Kudu? Gaskiya Ta Fito

Sojoji Na Nuna Wariya Wurin Fifita Sojojin Arewa Kan ’Yan Kudu? Gaskiya Ta Fito

  • Dakarun sojojin Najeriya sun karyata jita-jitar cewa suna nuna wariya a shari’ar da ake yi bayan gurfanar da sojoji a jihar Enugu
  • Rundunar ta bayyana haka ne yayin da ta ke martani kan cewa ana fifita sojoji daga Arewa kan takwarorinsu na Kudu
  • Daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu shi ya bayyana haka a cikin wata sanarwa da ya fitar inda ya yi fatali da jita-jitar

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

FCT, Abuja – Rundunar sojojin Najeriya ta yi martani kan jita-jiar nuna wariya a shari’ar sojoji tsakanin 'yan Kudu da Arewa.

Dakarun sojojin sun karyata jita-jitar cewa suna fifita sojoji daga Arewacin Najeriya kan takwarorinsu na Kudancin kasar.

Kara karanta wannan

Karin kudin wuta: Kano da sauran jihohi 12 da suka shirya inganta wuta ga al'ummarsu

Sojoji sun yi martani kan zargin nuna wariya tsakanin sojojin Arewa da Kudu
Rundunar sojoji ta karyata zargin nuna wariya tsakanin sojojin Kudu da Arewa. Hoto: HQ Nigerian Army.
Asali: Twitter

Wane zargi ake yi kan rundunar sojojin?

Hakan ya biyo bayan zargin cewa hukumar ta na nuna wariya a shari’ar da ake yi a jihar Enugu inda ta ke hukunta ‘yan Kudu tare da yin sassauci ga sojoji a Arewa.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da daraktan hulda da jama’a na rundunar, Onyema Nwachukwu ya bayyana a shafin Facebook.

Nwachukwu ya ce rundunar sojojin kasar an kirkire ta ne domin ‘yan kasa baki daya ba tare da nuna wani bambancin addini ko kabilanci ba.

Ya ce an samu korafe-korafe daga wasu sojoji wadanda aka gurfanar da su a gaban kotu.

Rundunar ta bayyana yawan 'yan Kudu a kotun

Ya kara da cewa an yi ta yada labarin ne domin kawo cikas a kokarin da rundunar ke yi a kasar na yaki da ta’addanci.

Kara karanta wannan

Sojoji sun kashe dumbin 'yan bindiga a jihohi 2 na Arewa, sun lalata sansaninsu

Nwachukwu ya ce mafi yawan alkalan kotun kusan kaso 60 daga Kudancin kasar suka fito yayin da shugaban kotun ya fito daga Arewa.

Ana yawan korafe-korafe a Najeriya kan rundunar kama daga daukar aiki da raba mukamai da kuma karin girma.

Sojoji sun bayyana ‘yan ta’adda da suka hallaka

A baya, kun ji cewa rundunar sojoji a Najeriya ta fitar da jerin sunayen sojoji da suka hallaka a Arewacin Najeriya.

Rundunar ta bayyana haka ne a cikin wata sanarwa da ta fitar inda ta ce ta samu nasarar ce kan irin hadin kai da take samu daga al’umma.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.