Musulmai Ba ’Yan Ta’adda Bane, Babban Malamin Addini Ya Soki Boko Haram, Ya Wanke Musulmai

Musulmai Ba ’Yan Ta’adda Bane, Babban Malamin Addini Ya Soki Boko Haram, Ya Wanke Musulmai

  • Babban Shugaban cocin RCCG Fasto Enoch Adeboye ya yi tsokaci kan shugabannin kungiyar Boko Haram da ke ikirarin cewa su Musulmi ne
  • Adeboye ya ce da'awar Boko Haram cewa su Musulmai ne ba ua nifin kowanne Musulmi dan ta'adda a duniya
  • Shahararren malamin ya ce hakan ya shafi malamin coci da matarsa da ba sa kula da mambobinsu

Jihar OgunBabban Babban Shugaban Cocin Redeemed Christian Church of God (RCCG) Fasto Enoch Adeboye, ya ce ikrarin da 'yan Boko Haram ke yi cewa su Musulmi ne ba ya nufin kowane Musulmi ya zama dan ta’adda.

Adeboye ya kuma ce don wani malamin addinin Islama ya ce a kashe uwargidan shugaban kasa, Oluremi Tinubu, hakan bai nufin kowane ya zama masheki.

Kara karanta wannan

Emefiele: Shugaba Tinubu ya kawo ƙarshen bincike a babban banki CBN, ya ɗauki mataki

Fasto ya ce Musulmai ba 'yan ta'adda bane
Fasto ya ce Musulmai ba 'yan ta'adda bane, ya fadi dalili | Hoto: Pastor Enoch Adeboye
Asali: Facebook

Duk Musulmi ba dan ta'adda bane, in ji fasto

Kamar yadda SaharaReporters ta ruwaito, malamin ya bayyana haka ne a wani wa'azi a ranar Juma’a 5 ga Afrilu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

“Ina so in yi muku wasu tambayoyi. Kasancewar shugabannin Boko Haram Musulmai ne ko kuma suna da'awar cewa su Musulmi ne, hakan yana nufin kowane Musulmi dan ta'adda ne?
“Saboda kawai wani malamin addinin Musulunci ya ce su kashe uwargidan shugaban kasanmu; shin hakan yana nufin kowane malami masheki ne?"

Ba kowane fasto ne mai aikin Allah ba

Da yake karin bayani, Adeboye ya buga misali ga al’ummar Kirista, inda ya bayyana cewa rashin hali mai kyau na malamin coci da matarsa bai nufin kowane malamin coci yana da mugun hali.

Jaridar Vanguard ta ruwaito malamin na karin bayani:

“Akwai wani mutum mai suna HUSPUPPY, wanda kasurgumin dan 419 ne da aka kama a Dubai. Kasancewarsa dan Najeriya, hakan yana nufin kowane dan Najeriya dan 419 ne?"

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

Coci ya tausayawa al'umma

A wani labarin, cocin RCCG ya bude kasuwa na musamman domin siyar da kaya cikin farashi mai rahusa.

Wannan lamari dai ya auku ne a jihar Kebbi, inda aka bayyana sunan kasuwar da ake yin wannan garabasa.

Shugaban cocin, Fasto Anthony Obinna-Ibe ya ce sun yi hakan ne domin samun rangwame na tsadar kaya da ake ciki.

Asali: Legit.ng

Authors:
Salisu Ibrahim avatar

Salisu Ibrahim (Head of Hausa Desk) Salisu holds BSc in IT (IOU, 2021) and is AfricaCheck's ambassador. He brings over five years of experience in writing, publishing and management. Trained by prestigious newspapers like Reuters, AFP, and Solutions Journalism Network, he curates news stories for the Hausa-speaking audience. He rose from Hausa Editor to Head of Desk at Legit. His commitment to excellence has earned him recognition, including the 2021 Best Hausa Editor award and the Legit Fearless Team Player of the Year 2023.