Adadin Mutanen da Aka Kashe a Harin Kogi Ya Karu, an Roki Tinubu Ya Dauki Mataki
- Rahotanni sun bayyana cewa adadin mutanen da suka mutu a harin 'yan bindiga a Kogi ya karu zuwa 25
- Chief Elias Atabor, shugaban al'umar Agojeju-Odo da ke karamar hukumar Omala ya bayyana wannan adadin
- Atabor ya roki Shugaba Bola Tinubu da ya kafa sansanin sojoji a Omala domin rage hare-haren 'yan bindiga
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Kogi - Chief Elias Atabor, shugaban al'umar garin Agojeju-Odo da ke Kogi, ya roki gwamnati da ta samar da sansanin sojoji a karamar hukumar Omala.
A cewar Atabor, samar da sansanin zai taimaka wajen rage yawan hare-haren da 'yan bindiga ke kaiwa garuruwan dake yankin.
"An kashe mutane 25" - Atabor
Atabor ya yi wannan rokon ne a zantawarsa da kamfanin dillancin labarai na ƙasa (NAN) a Lokoja a ranar Juma'a.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Shugaban al'umar ya ce:
" Muna fargabar cewa adadin waɗanda suka mutu zai ci gaba da ƙaruwa"
Jaridar Daily Trust ta rahoto cewa ya zuwa yanzun an gano cewa adadin mutanen da suka mutu a harin da 'yan bindiga suka kai garin ya haura zuwa 25 daga 19.
Rokon Atabor ga Shugaba Tinubu
Akwai ƙananan yara hudu a cikin wadanda suka mutu yayin da wasu da dama suka jikkata, kamar yadda jaridar.
Atabor ya ce:
"Muna rokon gwamnati ta samar mana da sansanin sojoji wanda zai taimaka mana wajen rage hare-haren'yan bindiga.
A lissafa garuruwan da ta'addancin ya fi shafa da suka hada da Agojeju-Odo, Ajokpachi-Odo da Bagaji.
"Gwamnati ta kawo mana dauki" - Ibrahim
Jaridar The Guardian ta kuma rahoto wani mai ruwa da tsaki a garin, Mr Ademu Ibrahim, ya roki Shugaba Bola Tinubu da Gwamna Ododo da su kai masu ɗauki.
Ya bayyana cewa 'yan bindigar sun lalata masu amfanin gona tare da yi wa 'yan uwansu kisan gilla, a domin haka ne suke neman taimako.
Ibrahim ya ce sun samu rahotanni na rikicin da ake yi tsakanin kungiyoyin daba a wasu sassa na Benue, fadan da ya zo ya shafe su kenan.
Yan bindiga sun kai hari Kogi
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa akalla mutane 19 'yan bindiga suka kashe a harin tsakar rana da suka kai Kogi.
Sun kaddamar da harin ne a ranar Alhamis a garin Agojeju-Odo da ke karamar hukumar Omala, a jihar.
Asali: Legit.ng