Ramadan: Gwamnan Arewa Ya Dakatar da Kwamishina a Jiharsa, Ya Fadi Dalili
- Gwamna Umar Namadi na jihar Jigawa ya dauki mataki kan wani kwamishina a jihar kan zargin badakalar kayan Ramadan
- Gwamnan ya dakatar da kwamishinan kasuwanci, Alhaji Aminu Kanta saboda zargin karkatar da kudin al'umma
- Kakakin ofishin sakataren gwamnatin jihar, Isma'il Ibrahim shi ya bayyana haka ga manema labarai a yau Juma'a 5 ga watan Afrilu
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Jigawa - Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya dakatar da kwamishina a gwamnatinsa kan zargin badakalar kudi.
Namadi ya dakatar da kwamishinan kasuwanci, Alhaji Aminu Kanta kan zargin karkatar da kudi a shirin rabon kayan tallafin Ramadan.
Musabbabin dakatar da kwamishinan Jigawa
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da kakakin ofishin sakataren gwamnatin jihar, Isma'il Ibrahim ya fitar, a cewar rahoton Tribune.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ibrahim ya tabbatar da haka ga manema labarai inda ya ce ana zargin kwamishinan da badakala da kayan Ramadan a karamar hukumar Babura.
"An dakatar da kwamishinan kasuwanci, Alhaji Aminu Kanta kan badakala a shirin rabon kayan Ramadan na karamar hukumar Babura."
"Dakatarwar na cikin wata sanarwa da sakataren gwamnatin jihar, Bala Ibrahim ya sanyawa hannu."
- Isma'il Ibrahim
Himmatuwar gwamnan wurin kwatanta gaskiya
Isma'il Ibrahim ya tabbatar da cewa hakan na daga cikin himmatuwar gwamnan jihar wurin tabbatar da gaskiya a harkokin gwamnati, kamar yadda SolaceBase ta tattaro.
Kanta kamar yadda rahotanni suka tabbatar aboki ne na kusa ga tsohon gwamna jihar, Muhammad Badaru Abubakar.
Badaru Abubakar shi ne Ministan tsaron Najeriya wanda Shugaba Tinubu ya nada shi bayan hawa karagar mulkin kasar a ranar 29 ga watan Mayun 2023.
Gwamna Namadi ya gwangwaje maniyyatan jiharsa
A baya, mun ruwaito muku cewa Gwamnan jihar Jigawa, Umar Namadi ya ba da gudunmawa ga maniyyatan jiharsa domin rage musu radadi a halin da ake ciki.
Namadi ya ware tallafin N1m ga kowane maniyyaci a jihar domin ganin sun iya biyan kudin kujerar hajji da aka kara.
Wannan na zuwa ne bayan hukumar alhazai ta kasa, NAHCON ta kara kudin kowace kujera a Najeriya da N1.9m.
Asali: Legit.ng