Gwamnati Ta Ce Za Ta Kuma Kara Kudin Wutar Lantarki, Ta Fadi Dalili
- Gwamnatin tarayya ta ce akwai shiri na kara kudin wutar lantarki bayan da ta sanar da karin kudin ga kwastomomi 'yan layin BAND A
- Ministan makamashi, Adebayo Adelabu, ya ce gwamnati ba za ta iya ci gaba da biyan tallafin wutar lantarki ba saboda yawan kudin
- A zantawarsa da Legit Hausa, Janare Bature daga jihar Katsina, ya ce talaka zai amfana idan wuta ta wadata ko da an kara kudin wutar
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Abuja - Kwanaki biyu bayan da hukumar kula da wutar lantarki ta Najeriya (NERC) ta sanar da karin kudin wuta ga kwastomomi 'yan BAND A, yanzu kuma ƙarin zai shafi har talaka.
Da yake jawabi ga manema labarai a Abuja a ranar Juma'a, ministan makamashi, Adebayo Adelabu ya ce ƙarin kudin na daga cikin shirin gwamnati na janye tallafin wutar lantarki.
Jaridar Daily Trust ta ruwaito shi yana cewa gwamnati za ta janye dukkanin tallafin lantarki ne saboda ba 'yan kasuwa damar saka hannun jari a harkar wutar.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Me zai jawo karin kudin lantarki?
Ministan ya ce:
"Mun yanke shawarar karin kudin ne domin aiwatar da tsarinmu na tabbatar da cewa wuta ta wadata ta hanyar tsayuwa da kafafunta ba da tallafin gwamnati ba.
"Tun farko mun dan tsahirta daga janye tallafin wutar lantarki lokaci daya kamar yadda aka yi wa fetur da gas saboda muna duba halin da 'yan Najeriya za su iya shiga."
Sai dai ministan ya ce lokaci ya yi da ya kamata gwamnati ta dauki mataki na magance matsalar wutar lantarki, ta hanyar janye tallafin a hankali, kamar yadda ta fara da 'yan BAND A.
Ministan ya kuma ce ƙarin da aka yi na baya bayan nan daga N66 zuwa N225 kadan ne idan aka kwatanta da kudin da suke kashewa wajen sayen fetur ko dizal.
Kudin tallafin lantarki ya yi yawa?
Jaridar The Citizen ta rahoto Adelabu ya yi bayanin cewa gwamnati ce ke biyan kaso 67% na kudin wutar da 'yan Najeriya ke sha, kama daga samar da ita, raba ta zuwa ga jama'a da sauran wahalhalu.
"Idan muka ce a tafi a haka, to gwamnati za ta biya akalla Naira tiriliyan 2.9 a shekarar 2024, wannan ya kwashe kusan kaso 10% na kasafin kasar.
"Ta ya zan tunkari gwamnati na ce ta biya wadannan kudin na tallafin lantarki alhali akwai manyan matsaloli a gabanta, dole sai mun yi nazari sosai."
- Adebayo Adelabu
"Akwai fa'ida amma za a wahala" - Janare
A zantawarsa da Legit Hausa, Janare Bature daga jihar Katsina, ya ce akwai fa'ida a karin kudin wutar lantarki.
Sai dai Bature ya ce talaka ba zai fahimci hakan ba a yanzu, kuma ƙarin kuɗin zai jefa masu karamin karfi cikin mawuyacin hali da farko.
Ya ce idan har wutar lantarki ta wadata ga talaka, zai zamana cewa sana'o'i sun yawaita, hanyar samun arziki ta karu.
A cewar shi rashin wadatacciyar wuta ya jawo kamfanoni da dama sun durkushe, sana'o'i sun tsaya, wanda ya tilasta mutane da yawa rasa ayyukansu.
Bature ya yi kira ga gwamnati da ta kara wa'adin da ta dauka na janye tallafin wutar lantarki gaba daya, ya ce har yanzu talaka bai farfaɗo daga matsin tattali ba.
An hana Tinubu janye tallafin lantarki
Tun da fari, Legit Hausa ta ruwaito cewa majalisar dattawa ta gargadi shugaban kasa Bola Ahmed Tinubu da ya jingine kudurinsa na janye tallafin wutar lantarki.
Sanata Aminu Iya Abbas ya ce bai kamata gwamnati ta ce za ta janye tallafin ba la'akari da cewa kasar na fuskantar matsin tattalin arziki.
Ya ce janye tallafin zai kara kudin wutar wanda kuma talaka ba zai iya biya ba kamar dai yadda ta faru bayan janye tallafin man fetur.
Asali: Legit.ng