Ana Fama da Tsadar Rayuwa, Dan Majalisar APC Ya Gwangwaje ’Yan Mazabarsa
- Dan majalisar tarayya na APC ya yi wa 'yan mazabarsa ta Egbeda/Ona Ara sha tara ta arziki a wannan lokaci na tsadar rayuwa da ake ciki
- Dan majalisar mai suna Hon. Amin Alabi, daga jihar Oyo, ya raba wa 'yan mazabar tasa injinan markade, janareta da kuma kayan abinci
- Alabi ya ce tallafin ya zama wajibi ne la'akari da halin matsin tattali da kasar ke cikin yana mai cewa tallafin zai bunkasa rayuwar jama'arsa
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Sani Hamza, kwararren edita ne a fannin nishadi, al'amuran yau da kullum da kuma siyasa. Sani yana da shekaru sama da biyar a aikin jarida
Jihar Oyo - Dan majalisar tarayya na APC da ke wakiltar mazabar Egbeda/Ona Ara a jihar Oyo, Hon. Amin Alabi, ya yi wa al'ummar mazabarsa sha tara ta arziki.
Dan majalisa ya raba injin markade
Jaridar The Nation ta ruwaito cewa Alabi ya raba wa 'yan mazabarsa janareta, injinan markade da kayan abinci, lamarin da ya saka farin ciki a zukatansu.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Wannan tallafi, a cewar Alabi, zai bunkasa tattalin arzikin al'ummar mazabarsa, tare da basu damar dogaro da kawunansu a wannan tsadar rayuwa da ake ciki.
Da yake jaddada muhimmancin al'umma su koma sana'o'in dogaro da kai, Alabi ya ce akwai bukatar hadin kai daga 'yan mazabar ta sa domin samun ci gaba.
'Yan mazabar Alabi sun yi godiya
Alabi ya wallafa a shafinsa na X cewa:
Tallafa wa al'umar mazaba ta yana daya daga cikin abubuwan da na fi so a aikina. Ina bayar da tallafin ne ta hanyoyi daban-daban, ya danganta da irin buƙatar da na ga al'uma tana da ita.
"Wasu 'yan mazabar na buƙatar kwamfutar tafi-da-gidanka. Wasu suna buƙatar firiza, wasu kuma suna buƙatar ka yi masu jagora wajen samun wani aiki. A jiya ma dai na yi wa al'uma ta aiki.
Karanta jawabin a nan kasa:
A jawaban su na godiya, wadanda suka ci gajiyar wannan tallafi, sun nuna cewa kayayyakin da aka raba masu za su taimaki rayuwarsu.
Dan majalisa a Kano ya raba tallafi
A wani labarin daga jihar Kano, dan majalisar NNPP mai wakiltar mazabar Fagge, Mohammed Bello Shehu, ya tallafa wa dalibai 512 da kudin makaranta.
Daga cikin wadanda aka ba tallafin, akwai dalibai daga jami'ar ABU Zariya, Usmanu Danfodiyo, Sokoto, FUD Jigawa da sauran makarantu.
Asali: Legit.ng