Wani dan majalisa a Arewa yayi wa mazabar sa sha tara ta arziki (Hotuna)

Wani dan majalisa a Arewa yayi wa mazabar sa sha tara ta arziki (Hotuna)

- Honarabul Abdulmalik Zubairu (Zannan Bungudu) dan majalisa daga jihar Zamfara mai wakiltar Maru da Bungudu a majalisar wakilai ta tarayya, ya bada tallafin;

- Motoci 21, Babura 503, Kekunan Dinki 250, Keke Napep 20, Injinin nika 50 da kuma Mutum 271 Kuddin jari.

Jimla mutum 1115 sune suka amfana da wannan tallafi.

Legit.ng ta samu labarin Honarabul Zanna ya bada tallafin ne ga al’ummar da suka fito daga yankinsa na Maru da Bungudu domin su samu sana’ar yi su kuma dogara da kansu, su taimaki kansu, iyalansu da ‘yan uwa da abokan arziki.

Wani dan majalisa a Arewa yayi wa mazabar sa sha tara ta arziki (Hotuna)
Wani dan majalisa a Arewa yayi wa mazabar sa sha tara ta arziki (Hotuna)

KU KARANTA: An kama barayi a cikin jirgi

Legit.ng ta samu a wani labarin kuma cewa a wani labarin kuma, Babbar Kotun Lagos ta bada umarni na karshe na kwace wasu kudaden kasar Naira kusan miliyan 450 da aka samu a wani shago na ‘yan chanji dake Lagos, kasancewar har yanzu babu wanda ya zo karban kudaden.

Mai sharia Rilwan Aikawa ya bada wannan umarni bayan ya saurari bayanai daga masu shigar da kara wato Hukumar EFCC.

Ku ci gaba da bin mu a Facebook: https://www.facebook.com/naijcomhausa da

Kuma Tuwita: http://twitter.com/naijcomhausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel