Sojoji Sun Fitar da Sunayen Hatsabiban 'Yan Bindiga da Suka Hallaka, Sun Fadi Adadi
- Dakarun tsaron Najeriya sun bayyana irin nasarorin da suka samu a yaki da ta'addanci a Arewacin Najeriya
- Rundunar ta fitar da jerin sunayen hatsabiban 'yan bindiga da ta hallaka daga watan Janairu zuwa Maris
- Daraktan yada labaran rundunar, Manjo-janar Edward Buba shi ya tabbatar da haka ga manema labarai a yau
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
FCT, Abuja - Rundunar tsaro ta fitar da jerin sunayen kasurguman 'yan bindiga da ta hallaka a bata-kashi da suka yi.
Rundunar ta fitar da sunayen ne a yau Alhamis 4 ga watan Afrilu a samame da ta yi tsakanin watan Janairu zuwa Maris.
Yawan 'yan bindiga da sojoji suka hallaka
Wannan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da darektan yada labaran rundunar, Manjo-janar Edward Buba ya fitar ga manema labarai a cewar Vanguard.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Buba ya ce a yanzu haka an yi nasarar hallaka mutane, 2,351, an kama 2,308 sai kuma an ceto wadanda aka yi garkuwa da su guda 1,241.
Ta bayyana cewa an yi nasarar hallaka kwamandojin 'yan ta'addan ne a yayin samame da suka yi a yankin Arewacin Najeriya.
Wasu daga cikin 'yan bindiga da aka hallaka
Daga cikin wadanda aka yi ajalin nasu akwai Abu Bilal Minuki da aka fi sani da Abubakar Mainok wanda shi ne shugaban ISWAP da Haruna Isiya Boderi.
Boderi ya kasance hatsabibin ɗan ta'adda da ya addabi dajin Birnin Gwari a Kaduna da kuma hanyar Abuja.
Sauran sun hada da Kachallah Damina da aka hallaka a ranar 24 ga watan Maris din wannan shekara, cewar Daily Post.
Rundunar ta yi nasarar hallaka shi da wasu mayaƙansa 50 da Kachallah Alhaji Dayi da Kachallah Idi.
Sai kuma Kachallah Kabiru da Kachallah Azarailu (Farin-Ruwa) da Kachallah Balejo da Alhaji Baldu da sauransu.
Sojoji sun hallaka kasurgumin ɗan bindiga
Kun ji cewa rundunar sojoji ta yi nasarar hallaka hatsabibin ɗan bindiga, Junaidu Fasagora a jihar Zamfara da ke Arewacin Najeriya.
Fasagora ya addabi yankin Arewa maso Yamma musamman yankunan karkara kafin sojojin su yi nasarar yin ajalinsa.
Asali: Legit.ng