'Yan Bindiga Sun Tarwatsa Ƙauyuka 551, Sun Raba Mutane 289,375 da Gidajensu a Jihar Arewa
- Ƴan bindiga sun raba mutane sama da 200,000 da muhallansu a yankunan kananan hukumomi 12 na jihar Kaduna
- Gwamnatin Kaduna karkashin Malam Uba Sani ta ce mutane 289,375 ne suka gudu suka bar gida a garuruwa 551 saboda matsalar tsaro
- Shugaban hukumar ba da agajin gaggawa (KADSEMA), Usman Mazadu, ya yabawa Uba Sani bisa ware kuɗin tallafawa mutanen
Ahmad Yusuf, kwararren edita ne a Legit Hausa da ya shafe tsawon shekaru yana kawo muku rahotannin siyasa, nishadi da al'amuran yau da kullum
Jihar Kaduna - Gwamnatin jihar Kaduna ta ce ‘yan bindiga sun raba mutane 289,375 da gidajensu a garuruwa 551 a fadin kananan hukumomi 12 na jihar.
Shugaban hukumar bada agajin gaggawa ta jihar Kaduna (KADSEMA), Usman Mazadu ne ya bayyana haka a wurin rabon kayan tallafi ga masu karamin karfi a Marabar Kajuru ranar Laraba.
Mazadu ya yi takaitaccen bayani kan matsalar ƴan bindiga da aka jima ana fama da ita a Kaduna, ya buga misali da Chikun, inda mutane 26,345 suka rasa gidajensu a kauyuka 134.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Ya ƙara da cewa a ƙaramar hukumar Birnin Gwari, mutane 70,893 suka bar gidajensu a kauyuka 84 saboda hare-haren ƴan bindiga, Premium Times ta rahoto.
"Wannan ƙididdiga ita ke wakiltar rayuka, buri, da juriyar mutanenmu. Garuruwa 551 lamarin ƴan bindiga ya shafa kuma an raba mutane 289,375 da muhallansu a ƙananan hukumomi 12.
- Usman Mazadu.
Gwamna Sani ya ware kuɗin tallafi
Mista Mazadu ya yabawa Gwamna Uba Sani na jihar Kaduna bisa ware Naira biliyan 11.4 ga shirin tallafawa wadanda abin ya shafa.
Ya kara da cewa "Muna mika godiyar mu ga mai girma gwamna saboda yadda ya nuna kulawarsa."
Shugaban KADSEMA ya ce tallafin zai isa ga dukkan waɗannan yankuna da ke ƙananan hukumomi 12 daga nan zuwa mako biyu masu zuwa.
Mataimakiyar gwamnan jihar, Hadiza Balarabe, wadda ta samu wakilcin shugaban ma’aikatanta, James Kanyip, ta ce gwamnati ta tashi tsaye wajen ganin ta kawar da ƴan bindiga.
Ya nanata ƙudirin Gwamna Sani na bayar da tallafin da ya kamata ga wadanda rikicin rashin tsaro ya shafa, rahoton This Day.
An ceto yara 30 a Katsina
A wani rahoton na daban Ƙananan yara 30 da ƴan bindiga suka sace a kauyen Kasai da ke yankin ƙaramar hukumar Batsari a jihar Katsina sun shaƙi iskar ƴanci.
Mai magana da yawun rundunar ƴan sandan Katsina, ASP Abubakar Sadiq, ya ce masu ruwa da tsaki a yankin sun taimaka wajen ceto yaran.
Asali: Legit.ng