Ramadan: Abba Kabir Ya Yi Zazzafan Gargadi Kan Rabon Kayan Tallafi Karo Na 4 a Kano

Ramadan: Abba Kabir Ya Yi Zazzafan Gargadi Kan Rabon Kayan Tallafi Karo Na 4 a Kano

  • Gwamnan jihar Kano, Abba Kabir Yusuf ya shirya sake rabon kayan tallafi a watan Ramadan a karo na hudu a jihar
  • Gwamna Abba Kabir ya yi gargadi mai tsauri kan masu karkatar da kayan inda ya ce ba za su ji da dadi ba
  • Legit Hausa ta ji ta bakin tsohon ɗan takarar majalisar dokoki a jami'yyar PDP a Kano kan yadda ake rabon kayan tallafin

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Kano - Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya tura sakon gargadi ga masu son kawo cikas a rabon kayan tallafi a jihar.

Abba Kabir ya yi wannan gargadin ne yayin kaddamar da rabon kayan tallafin karo na hudu a Kano.

Kara karanta wannan

Bayan Kaduna, Gwamnan APC ya zargi uban gidansa da yashe lalitar gwamnati gaba ɗaya

Abba Kabir ya sake kaddamar da rabon kayan tallafi a karo na 4, ya yi gargadi
Abba Kabir ya gargadi masu karkatar da kayan tallafi da su guji fushin hukuma a Kano. Hoto: Abba Kabir Yusuf.
Asali: Facebook

Wane mataki Abba Kabir zai dauka?

Gwamnan ya ce zai dauki mummunan mataki kan wadanda ke shirin karkatar da kayan don biyan bukatar kansu.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya bukaci yin adalci a rabon kayan domin tabbatar da ya isa wurin wadanda aka yi dominsu a jihar, a cewar Daily Trust.

An kaddamar da rabon kayan ne domin zagaye dukkan ƙananan hukumomi 44 da ke fadin jihar baki daya.

Yawan abinci da za a raba a Kano

Gwamnan Kano ya sanar da rabon buhunan shinkafa 112,220 masu nauyin kilo 25 ga gidaje musamman na marasa hali a jihar.

Abba Kabir ya ce za a fara rabon kayan ne daga yankin Kano ta Kudu kafin ci gaba da rarraba kayan ga sauran yankunan jihar.

Ana sa ran wannan tallafi sai taimakawa akalla gidaje 224,440 a jihar musamman ga mabukata domin samun sauƙi a watan Ramadan.

Kara karanta wannan

Kano: Ganduje ya shiga sabuwar matsala yayin da Abba Gida-Gida ya dauki matakin bincike

Kafin fara rabon kayan, gwamnan ya zagaya domin ganewa idonsa yanayin kyawun shinkafar da za a raba, cewar rahoton Leadership.

Tattaunawar Legit Hausa da jigon PDP a Kano

Legit Hausa ta ji ta bakin tsohon ɗan takarar majalisar dokoki a jami'yyar PDP a Kano kan yadda ake rabon kayan tallafin

Adnan Mukhtar Tudun Wada ya koka kan yadda ake rabon cikin rashin adalci tare da nuna wariyar siyasa.

"Gaskiya ba mu jin dadin yadda ake rabon kayan tallafi saboda lokacin siyasa ya wuce, ita gwamnatin ta kowa da kowa ne."
"Duk da cewa ta na yin rabon tallafin a lokacin da ya kure, abincin da ake rabawan ma ba shi da inganci."
"Gwamnatin ta riga ta ware 'yan jam'iyya 'yan Kwankwasiyya su kadai ta ke ba tallafin, a mazaba ta idan aka ba wani tallafin cewa ake an ba makiyin, ko aiki ne yanzu idan ba ka gwamnatin zai yi wahala ka samu."

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

- Adnan Mukhtar

Abba ya haramta fina-finan 'yan daba

Mun kawo muku labarin cewa Gwamna Abba Kabir na jihar Kano ya ba da sabon umarni ga masu shirya fina-finai a masana'antar Kannywood.

Gwamna ya dakatar da su daga shirya fina-finai da ke ɗauke da 'yan daudu da kuma 'yan daba a jihar.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.