Buhari Ya Kadu Bayan Rasuwar Tsohon Shugaban NLC, Ya Fadi Amfanin da Ya Yi Masa

Buhari Ya Kadu Bayan Rasuwar Tsohon Shugaban NLC, Ya Fadi Amfanin da Ya Yi Masa

  • Yayin da ake cikin jimamin mutuwar tsohon shugaban kungiyar NLC, Ali Chiroma, tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna alhini
  • Buhari ya bayyana marigayin a matsayin mutum mai tsantseni ganin yadda ya gudanar da shugabancin kungiyar ba tare da tsoron komai ba
  • Tsohon shugaban ya ce tabbas an tafka babban rashin mutum wanda ya ba da gudunmawa sosai a bangaren tattalin arziki da kuma kungiyar NLC

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Jihar Borno - Tsohon shugaban kasa, Muhammadu Buhari ya nuna alhini kan rasuwar tsohon shugaban kungiyar NLC, Ali Chiroma.

Buhari ya bayyana kaduwarsa kan rashin Chiroma inda ya ce tabbas an tafka babban rashi a jihar Borno da Najeriya.

Kara karanta wannan

Gwamnan PDP ya ɗauki zafi kan rikicinsa da ministan Tinubu, ya faɗi dalilin amincewa da sulhu

Buhari ya tura sakon jaje bayan rasuwar tsohon shugaban NLC
Muhammadu Buhari ya nuna alhini bayan rasuwar tsohon shugaban NLC, Ali Chiroma. Hoto: Muhammadu Buhari, Ali Chiroma.
Asali: Facebook

Gudunmawar da marigayin ya bayar

Tsohon shugaban kasar ya bayyana haka ne a yau Laraba 3 ga watan Afrilu a shafinsa na X.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

Ya ce marigayin ya ba da gudunmawa a bangaren tattalin arzikin Najeriya da kuma kungiyar NLC.

Ya kara da cewa marigayin ya kasance shugaba marar tsoro wanda ya gudanar da shugabancin kungiyar ba tare da tsoron komai ba.

"Chiroma mutum ne mai tsantseni wanda zai yi wahala ka ci nasara a kansa, ya na da kwarewa kuma shugaba ne marar tsoro."
"Ya ba da gudunmawa mai tsoka a bangaren tattalin arzikin Najeriya da kuma shugabancin kungiyar NLC."
"Chiroma ya ba ni gudunmawa sosai a harkar siyasa ta inda ya kasance a matsayin mai goyon bayana kafin da kuma bayan kasancewata shugaban kasa."

- Muhammadu Buhari

Buhari ya jajantawa iyalan marigayin

Kara karanta wannan

Abin da Remi Tinubu ta fadawa matan tsoffin shugabannin Najeriya yayin buda baki

Tsohon shugaban ya kuma tura sakon jaje ga iyalan marigayin da kuma al'ummar jihar Borno gaba daya kan wannan babban rashi.

"Ina mika sakon jaje ga iyalan marigayin da gwamnatin jihar Borno da al'ummar Borno, ina addu'ar Allah ya ba su hakurin jure wannan babban rashi."

- Muhammadu Buhari

Tsohon shugaban NLC ya kwanta dama

A baya, mun baku labarin cewa tsohon shugaban kungiyar NLC, Ali Chiroma ya riga mu gidan gaskiya.

Marigayin ya rasu ne a jiya Talata 2 ga watan Afrilu a asibitin koyarwa na Jami'ar Maiduguri da ke jihar Borno.

Sakataren kungiyar 'yan jarida ta jihar Borno, Ali Ibrahim Chiroma shi ya sanar da mutuwar marigayin ga 'yan jaridu.

Asali: Legit.ng

Online view pixel