Kano: Abba Kabir Ya Ba Masu Shirya Fina Finai Sabon Umarni Domin Yaki da Rashin Tarbiyya
- Yayin da ake fama da rashin tarbiyya a jihar Kano, gwamnatin jihar ta dauki mataki kan masu shiryar fina-finai a jihar
- Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haramta shirya duk wani wasan kwaikwayo da ke ɗauke da 'yan daba ko kuma 'yan daudu
- Hakan bai rasa nasaba da yawan dabanci da ake samu a birnin Kano wanda ya jawo rasa rayuka da dama a kwanakin nan
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Kano - Gwamnatin jihar Kano ta kafa sabuwar doka ga masu shirya fina-finai a fadin jihar baki daya.
Gwamna Abba Kabir Yusuf ya haramta shirya fim da ke nuna dabanci ko kuma harkar 'yan daudu a jihar.
Yadda 'yan daba suka addabi Kano
Wannan mataki bai rasa nasaba da yawan ta'addanci da ake samu a tsakanin matasa a birnin Kano.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
A 'yan kwanakin nan an samu rasa rayuka da dama sanadin ayyukan 'yan daba a birnin Kano da kewaye.
Har ila yau, a Kano ana yawan samun 'yan daudu da ke kawo cikas musamman a kokarin hukumar Hisbah na gyara tarbiyya.
Abin da El-Mustapha ya ce kan matakin
Har ila yau, shugaban Hukumar tace fina-finai a Kano, Abba El-Mustapha ya tabbatar da daukar matakin a shafinsa na Facebook.
El-Mustapha ya ce sun dauki matakin ne biyo bayan korafe-korafen da al'umma ke yi kan shirya fina-finan dake nuna fadan Daba da harkar daudu a jihar Kano.
Abba El-mustapha ya bada wannan umarni ne jim kadan bayan ganawa da ya yi da manyan ma'aikatan Hukumar tace fina-finan na Kano
An haramta bude gidajen gala a Kano
A baya, mun ruwaito muku cewa Hukumar tace Fina-finai da Ɗab’i ta Jihar Kano ta umarci rufe dukkan gidajen gala a fadin jihar.
Shugaban hukumar a jihar, Abba El-Mustapha shi ya bayyana haka a ranar Lahadi 10 ga watan Maris a shafinsa na Facebook.
El-Mustapha ya ce an dauki wannan matakin ne saboda shirye-shiryen da ake yi na tunkarar watan azumin Ramadan.
Asali: Legit.ng