InnaliLlahi: Hadimin Gwamnan APC Ya Riga Mu Gidan Gaskiya da Shekaru 66
- An shiga jimami a jihar Ogun bayan hadimin gwamnan jihar, Dapo Abiodun ya rasu ya na shekaru 66 a duniya.
- Farfesa Joseph Odemuyiwa ya rasu ne a yau Talata 2 ga watan Afrilu bayan ya gamu da mummunan hatsarin mota
- Marigayin ya rike mukamin hadimin gwamnan a bangaren koyan sana’o’i inda aka kwatanta shi da mutum mai son ci gaban al’umma
Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ogun – Tsohon hadimin gwamnan jihar Ogun, Dapo Abiodun ya rasu bayan ya gamu da mummunan hatsarin mota.
Marigayin Farfesa Joseph Odemuyiwa ya rasa ransa ne a yau Talata 2 ga watan Afrilu a kan hanyarsa ta zuwa Ibadan.
Yaushe marigayin ya rasu?
Tribune ta tattaro cewa dan Majalisar Remo ta Arewa a jihar, Dickson Awolaja shi ya tabbatar da mutuwar marigayin.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Dan Majalisar wanda ya fito yanki daya da marigayin ya ce Joseph ya rasu a kan hanyarsa ta zuwa garin Ibadan.
“Na samu labarin rasuwar Joseph daga abokinsa dazu-dazu, Farfesan ya rasu a kan hanyarsa ta zuwa Ibadan inda ya gamu da hatsarin mota.”
- Dickson Awolaja
Mukamin da ya rike a gwamnati
Farfesa Joseph mai shekaru 66 a duniya ya yi aiki a manyan makarantu mallakin jihar da suka hada da Jami’ar Olabisi Onabanjo.
Sauran sun hada da Jami’ar Ago Iwoye da kuma Jami’a ta tsangayar ilimi ta Tai Solarin a yankin Ijagun.
Odemuyiwa ya rike mukami a gwamnatin Dapo Abiodun na farko daga shekarar 2019 zuwa 2023, a cewar Vanguard.
Sai dai ba a dawo da shi ba bayan gwamnan ya yi nasara a karo na biyu bayan gudanar da zaben 2023.
Fitaccen Furodusa ya riga mu gidan gaskiya
Kun ji cewa shahararren furodusan fina-finan Nollywood a Najeriya ya riga mu gidan gaskiya ya na da shekaru 56 a duniya.
Marigayin Wole Oguntokun ya rasu ne bayan fama da jinya inda wani daga cikin abokan aikinsa, Peters ya tabbatar da mutuwarsa.
Wannan na zuwa ne bayan masana’antar Nollywood ta rasa jarumai a dan kankanin lokacin wadanda suka shahara.
Asali: Legit.ng