Halin Kunci: Coci Ya Tausayawa Al'umma, Ya Bude Kasuwa Domin Siyar da Kaya da Araha
- Yayin da ake cikin mawuyacin hali na tsadar rayuwa, coci ya bude kasuwa domin siyar da kaya a farashi mai rahusa
- Cocin Redeemed Christian a jihar Ekiti ya bude kasuwar ne a jiya Litinin 1 ga watan Afrilu a birnin Ado-Ekiti da ke jihar
- Za a rika cin kasuwar akalla sau biyu ko uku a shekara musamman ga mambobin cocin domin saukaka musu tsadar rayuwa
Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne a bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum ne, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.
Jihar Ekiti - Cocin Redeemed Christian ya bude kasuwa na musamman domin siyar da kaya cikin farashi mai rahusa.
Wani cocin RCCG da ke birnin Ado-Ekiti ya bude kasuwar mai suna 'Jesus Market' domin saukakawa mambobinsa, Punch ta tattaro.
Musabbabin bude kasuwar araha a Ekiti
Shugaban cocin, Fasto Anthony Obinna-Ibe ya ce sun yi hakan ne domin samun rangwame na tsadar kaya da ake ciki.
LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng
Anthony ya ce za a rika bude kasuwar ne sau biyu ko uku a kowace shekara domin yin harkokin cinikayya, cewar Igbo TV.
Faston ya bayyana haka ne yayin kaddamar da kasuwar a ranar Litinin 1 ga watan Afrilu a birnin Ado-Ekiti.
"Komai ya kara rikicewa, mutane ba su da kudin ciyar da kansu da sutura, mun yanke shawarar kaddamar da wannan tsari domin taimakon jama'a."
"Ya kamata masu hali su tausayawa talakawa, akwai wadanda ko abinci ba su da shi, wannan shi ne lokacin da ya dace a kula da su."
- Anthony Obinna-Ibe
Nau'in abinci da kaya da ake siyarwa
A kasuwar, mambobin cocin za su siya kayan cikin farashi mai sauki saboda halin da ake ciki a Najeriya.
Kudin gari da ake siyarwa N1,000 ya koma N400, sannan doya guda biyar a kan kudi N9,000 za a siyar N3,000 sai shinkafa mudu na N2,500 ya dawo N1,000.
Wike ya raba kayan abinci
Legit ta ruwaito muku cewa, Ministan Abuja, Nyesom Wike ya kaddamar da rabon kayan abinci ga al'ummar Musulmai a birnin.
Wike ya ce ya raba kayan ne domin saukakawa Musulmai musamman a wannan halin da ake ciki na tsadar rayuwa.
Asali: Legit.ng