Jerin Sabbin Gwamnonin Arewa 7 da Suka Karbi Bashin Biliyoyi Cikin Watanni 6 Kacal

Jerin Sabbin Gwamnonin Arewa 7 da Suka Karbi Bashin Biliyoyi Cikin Watanni 6 Kacal

Hukumar Kula da Bashi a Najeriya (DMO) ta bayyana yadda wasu sabbin gwamnoni suka karbi bashin biliyoyi a cikin watanni shida kacal.

Legit.ng Hausa ta bude tasha a manhajar Whatsapp. Kasance tare da mu don samun rahotanni da dumi-dumi!

Abdullahi Abubakar, Editan Legit Hausa ne ta bangaren siyasa, kasuwanci da al'amuran yau da kullum, ya na da gogewar aikin jarida sama da shekaru uku.

Hukumar ta ce a lokacin da aka karbi bashin farashin dala na N889 idan aka kwatanta da yanzu da ya kai fiye N1,000.

Gwamnonin Arerwacin Najeriya 7 da suka ciyo bashin biliyoyi a watanni 6
Gwamnonin Kano da Kaduna da Katsina da sauran jihohi 4 a Arewa da suka karbi bashin biliyoyi. Hoto: Uba Sani, Abba Kabir, Dikko Radda.
Asali: Facebook

Sabbin gwamnonin sun karbi bashin ne a gida da waje musamman daga Bankin Duniya da kuma hukumar IMF, cewar Tribune.

Legit Hausa ta jero muku jihohin da suka karbi bashin a Najeriya.

LURA: Shin kana son bamu labari da tattaunawa da marubutanmu? Tuntubemu a info@corp.legit.ng

1. Kano

Jihar Kano na daga cikin jihohi da ke samun kudin shiga ganin yadda ta ke da bunkasar tattalin arziki musamman a kasuwanci.

Kara karanta wannan

Hajj 2024: Gwamnan PDP ya biya rabin kuɗin da aka ƙarawa mahajjatan jihar Arewa, ya faɗi dalili

Gwamna Abba Kabir Yusuf ya karbi bashin $6.6m bayan hawansa mulki a watan Mayun 20023.

2. Kaduna

Gwamna Uba Sani a jihar Kaduna ya karbi bashin $17m daga wajen kasar Najeriya domin inganta jihar.

Wannan na zuwa ne bayan gwamnan ya zargi uban gidansa, Nasir El-Rufai da tara masa tulin bashi a jihar.

3. Zamfara

Jihar Zamfara ita ma ta karbo bashin akalla $655 da $563 daga Bankin Duniya a shekarar da ta gabat.

Gwamna jihar, Dauda Lawal Dare ya sake karbar bashin cikin gidan har N14bn.

4. Katsina

Hukumar DMO ta ce ana bin jihar Katsina bashin N36.94bn yayin da ya karu zuwa N62bn har zuwa N99.3bn a watan Disambar 2023, cewar TheCable.

5. Neja

Neja ta na gaba-gaba wurin cin bashi mai yawa inda bashin cikin gida da ake binta ya kai N17bn wanda ya karu zuwa N121bn a watan Yulin 2023 har zuwa N139bn a karhsen shekarar 2023.

Kara karanta wannan

Musulmai na murna yayin da gwamna Kirista ya biya cikon kudin kujerun Hajji ga maniyyata

6. Plateau

Gwamna Caleb Muftwang ya karbi bashin N16bn daga cikin gida yayin da ci bashin $831,008 daga ketare.

7 Sokoto

Sokoto ta karbi bashi daga ketare har $499,472 da kuma $472 daga Bankin Duniya.

7. Taraba

Gwamnan jihar Taraba, Kefas Agbu kuma a bangarensa ya karbi bashin $1.51m daga ketare domin inganta jihar.

Uba Sani ya yi korafi kan bashin Kaduna

Kun ji cewa Gwamna Uba Sani a jihar Kaduna ya yi korafi kan bashin da ya gada daga tsohuwar gwamnatin Nasir El-rufai.

Gwamnan ya ce tulin bashin da aka bar masa ya na cinye kudin da suke samu daga Gwamnatin Tarayya.

Wannan ikrari na gwamnan ya ta da jijiyoyin wuya musamman wadanda ke goyon bayan Nasir El-rufai, ciki har da 'dansa, Bello El-Rufai.

Asali: Legit.ng

Authors:
Abdullahi Abubakar avatar

Abdullahi Abubakar (Hausa editor) Marubuci kuma kwararren ɗan jaridan da ya shafe shekaru 3 yana rubutu a fannin siyasa da harkokin yau da kullum. Ya kammala digirin farko a jami'ar Maiduguri. Ya samu horon aikin jarida a Reuters da AFP, ya sha halartar tarukan karawa juna sani game da bincike da adabi. Tuntube shi a abdullahi.abubakar@corp.legit.ng.